An saki ‘yan jarida biyun da aka sace a Kaduna, Abdulgafar Alabelewe na jaridar The Nation da Abduraheem Aodu na jaridar Blueprint, tare da iyalansu. Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Kaduna ta tabbatar da wannan ci gaban a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.
Sanarwar, wadda Shugabar Ƙungiyar NUJ reshen Kaduna, Asma’u Yawo Halilu, ta sa hannu, ta nuna godiya ga duk waɗanda suka taimaka wajen ganin an sako ‘yan jaridar da iyalansu. Ta gode musamman ga ofishin CP, Jihar Kaduna, NSA, DG DSS, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Gwamnatin Jihar Kaduna, Shugaban NUJ, da duk ‘yan Nijeriya da suka yi addu’a don dawowarsu lafiya.
- Zargin Dokar Bai Wa Auren Jinsi Kariya: Gwamnatin Tarayya Ta Koka Kan Rahoton Wata Jarida
- Matar Dan Jaridar Da ‘Yansanda Suka Kashe A Kenya Ta Samu Diyyar Dala 78,000
Ƙungiyar ta bayyana cewa za su sanar da lokacin da za su tarbi ‘yan jaridar a Kaduna don murnar dawowarsu da kuma gode wa Allah.