• English
  • Business News
Sunday, September 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Majalisa Na Binciken Cibiyoyin Ci Gaban Masana’antu 30 Da Aka Yi Watsi Da Su

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
in Manyan Labarai
0
Ƴan Majalisa Na Binciken Cibiyoyin Ci Gaban Masana’antu 30 Da Aka Yi Watsi Da Su
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Majalisar Wakilai a ranar Talata, ta yanke shawarar yin bincike kan yadda aka yi watsi da cibiyoyin ci gaban masana’antu (IDC) sama da 30 a fadin kasar nan.

Majalisar ta umurci kwamitinta kan masana’antu da ya binciki yadda aka yi watsi da su tare da ba da shawarar yin amfani da cibiyoyin da suka dace don manufofinsu tare da bayar da rahoto cikin makonni hudu don ci gaba da aiwatar da doka.

  • NNPC Ta Gaza Halartar Zaman Binciken Majalisa Kan Ɓatan Naira Tiriliyan 210
  • Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma

Kudurin ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Onitsha ta Arewa/Kudu na Jihar Anambra, Hon. Emeka Idu, ya gabatar a zauren majalisa.

Idu ya lura cewa an kafa IDC sama da 30 a shekarun 1970 tare da manufar ba da taimako ga kanana da matsakaitan masana’antu.

Dan majalisar ya ce duk da cibiyoyin shiyya hudu da ke Osogbo, Owerri, Zariya da Maiduguri, ba za a iya cewa kasar ta ci gajiyar kafa su ba.

Labarai Masu Nasaba

Mun Tara Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau 

Boko Haram Ta Hallaka Mutane 61 A Jihar Borno

Ya kara da cewa, babban makasudin kafa cibiyoyin da kudaden jama’a shi ne bunkasa masana’antu, da rage bukatar musayar kudaden waje, da samar da fa’idoji masu yawa ga kasar nan.

Idu ya ce IDCs, musamman Cibiyoyin shiyyoyi hudu, sun cika da manyan injina don yada ilimin fasahar masana’antu da fasahar da za su yi tasiri matuka kan yunkurin kasar na samar da masana’antu.

Ya bayyana damuwarsa cewa, “A tsawon shekaru, kusan dukkanin IDCs, ma’aikata da kayan aiki a yi asarar su kuma wasu kayan aikin sun daina aiki.

“Duk da cewa gwamnatin tarayya ta mika wadannan cibiyoyi ga hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) tsawon wasu shekaru a yanzu, babu wani abin da aka yi gaba daya don gyara wadannan cibiyoyi a halin da ake ciki.

“Idan ba a duba wannan yanayin ba, kasar za ta ci gaba da rasa moriyar masana’antu, wanda hakan zai shafi yanayin rayuwar jama’a.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: majalisa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tinubu Ya Sasanta Wike, Fubara, Da Ƴan Majalisar Ribas

Next Post

Zaɓen 2027 Ya Fi Damun Tinubu Fiye Da Gudanar Da Shugabanci – Sanata Dickson

Related

Mun Tara Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau 
Manyan Labarai

Mun Tara Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau 

7 hours ago
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Hallaka Mutane 61 A Jihar Borno

19 hours ago
Mutanen Gari Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu A Sakkwato
Manyan Labarai

Mutanen Gari Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu A Sakkwato

22 hours ago
NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai
Manyan Labarai

NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai

1 day ago
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 2 Da Wasu 156 Kan Aikata Laifuka A Jigawa

2 days ago
Sojoji Sun Kwato Makamai Da Babura, Sun Ceto Mutane 3 A Kaduna 
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Ɗan Bindiga Ɗauke Da Makamai A Jihar Filato

2 days ago
Next Post
Zaɓen 2027 Ya Fi Damun Tinubu Fiye Da Gudanar Da Shugabanci – Sanata Dickson

Zaɓen 2027 Ya Fi Damun Tinubu Fiye Da Gudanar Da Shugabanci – Sanata Dickson

LABARAI MASU NASABA

Arewa

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Bullo Da Sabbin Matakan Yaki Da Ta’addanci

September 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

Kwamishinan ‘Yansandan Abuja Ya Gargadi Jami’ansa Kan Arangama Da Direbobi A Titi

September 7, 2025
Yin Ƙidaya Na Da Muhimmanci Ga Ci Gaban Al’umma – Kwamishina Sa’adatu

Yin Ƙidaya Na Da Muhimmanci Ga Ci Gaban Al’umma – Kwamishina Sa’adatu

September 7, 2025
ASUU

Malaman Jami’o’i Sun Zama Abin Tausayi —Kungiyar ASUU

September 7, 2025
Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu A Makarantun Nijeriya

Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu A Makarantun Nijeriya

September 7, 2025
Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63 

Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63 

September 7, 2025
Mun Tara Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau 

Mun Tara Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau 

September 7, 2025
Fyade

Matsalar Ciwon Kwakwalwa A Gidajen Yarin Kasar Nan

September 7, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Sake Maido Da Ma’aikatar Yaki A Amurka Ya Nuna Babu Dakatawa A Yaki Hatta A Wajen Sa Suna 

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Sake Maido Da Ma’aikatar Yaki A Amurka Ya Nuna Babu Dakatawa A Yaki Hatta A Wajen Sa Suna 

September 6, 2025
Rikicin NNPP A Kano: Wani Tsagi Ya Soki Korar Abdulmumini Jibrin Kofa

Rikicin NNPP A Kano: Wani Tsagi Ya Soki Korar Abdulmumini Jibrin Kofa

September 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.