A ranar Talata a Washington DC, da kwamitocin Majalisar Dokokin Amurka sun gudanar da taron haɗin gwiwa kan sace-sacen da ake yi da kuma zargin zaluntar Kiristoci a Nijeriya.
An gudanar da zaman ne bisa umarnin Shugaba Donald Trump, wanda a ranar 31 ga Oktoba ya umurci Kwamitin Kuɗin Gida na Majalisar Wakilai da ya binciki abin da ya bayyana a matsayin kisan Kiristoci a Nijeriya, sannan ya miƙa rahotonsu zuwa Fadar White House.
A gefe guda, Majalisar Wakilai ta Nijeriya za ta tattauna kan halin tsaro a ƙasar.
- Ci Gaban Fasahar AI A Kasar Sin Ya Nuna Gazawar Matakan Amurka Na Tare Hanyar Sin
- Ƴan Ta’adda Sun Sace Mata Manoma 13 A Borno
Zaman Majalisar Amurka, wanda Mataimakin Shugaban Kwamitin Kuɗin Gida da Shugaban Ƙaramin Kwamitin Tsaro na Ƙasa Mario Díaz-Balart ya jagoranta, ya haɗa mambobin Kwamitin Kuɗin Gida da Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Wakilai tare da ƙwararru kan ’yancin addini.
Cikin mahalarta taron sun haɗa da ’Yan Majalisa Robert Aderholt, Riley Moore, Brian Mast, Chris Smith, Shugabar Kwamitin ’Yancin Addini na Duniya na Amurka, Ɓicky Hartzler, Sean Nelson na Ƙungiyar Alliance Defending Freedom International, da Dr Ebenezer Obadare na Hukumar Hulɗa da Harkokin Waje.
Díaz-Balart ya fara taron da bayyana ’yancin addini a duniya a matsayin “wajibi na ɗabi’a da kuma muhimmin abin da Amurka ke buƙata.” Ya jaddada cewa “bai kamata kowa ya ji tsaro rayuwarsa don ya zaɓai yadda zai gudanar da ibada ba.”
Ya ce “ Yana da niyyar ci gaba da tsara manufofi da za su kare ’yancin mutum na rayuwa bisa addininsa ba tare da tsoro na tashin hankali ko ramuwar gayya ba.”
Díaz-Balart ya lura cewa kuɗin da aka ware a dokar kasafin kuɗi ta FY26 yana magance wannan alƙawari, kuma ya ƙara da cewa yana shirin ƙarfafa waɗannan ƙoƙarin ta hanyar wucewa da matakin kasafin kuɗi na shekara ɗaya, wanda ya bayyana a matsayi muhimmi wajen ci gaba da aiwatar da manufofin ‘America First’.
Aderholt ya nuna damuwarsa, inda ya bayyana halin da ake ciki a Nijeriya a matsayin “rikici da ba za a iya yin watsi da shi ba.”
Ya ce, “Dole ne mu tsaya tsayin daka tare da al’ummomin Kiristoci na Nijeriya da duk masu bin addini da ake zalunta a duniya baki ɗaya, kuma ina yaba wa ƙoƙarin haɗin gwiwarmu wajen ba Shugaba bayanan da ake buƙata don tunkarar wannan masifa mai ƙaruwa.”
Moore ya danganta taron da sabuwar sanarwar gwamnatin kan sake sanya Nijeriya a matsayin ƙasa mai damuwa ta musamman.
Ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta “ƙwace makaman waɗannan rundunonin, mayar da iyalan da aka tilasta musu barin gidajensu, sannan a gurfanar da masu laifin gaban shari’a.”
A jawabinsa, Shugaban Ƙaramin Kwamitin Harkokin Waje na Afirka na Majalisar Wakilai, Smith, ya bayyana Nijeriya a matsayin “Cibiya ta tashin hankalin addini,” yana cewa Kiristoci da Musulmai masu matsakaicin ra’ayi suna fuskantar “Barazanar kisa, fyaɗe, da azabtarwa a kowane lokaci.”














