Dele Momodu, sanannen ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa yawancin magoya bayan jam’iyyar sun fara ficewa daga cikinta, suna barin tsarin jam’iyyar a hannun ministan babban birnin tarayya. Dele ya bayyana hakan ne yayin wani shiri a Channels TV, inda ya nuna cikakken goyon bayansa ga sabon ƙawancen jam’iyyun adawa da suka rungumi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin fuskantar zaɓen 2027.
Momodu ya ce, duk da Wike yana PDP, kasancewarsa a gwamnatin APC na nuna rashin amanna kuma ya janyo rikici cikin jam’iyyar. A cewarsa, “mutane suna barin gawar PDP ga Wike da ƙawayensa kawai.” Ya zargi APC da shirya makirci na tura mutanenta cikin jam’iyyun adawa don rage musu ƙarfi a 2027, yana mai cewa APC na ƙoƙarin hana gasa mai tsabta a gaba.
- Tinubu Ya Sasanta Wike, Fubara, Da Ƴan Majalisar Ribas
- Duk Da Cewa Wike Ba Ɗan APC Ba Ne Amma Muna Jin Daɗin Aikin sa – Tinubu
Ya bayyana cewa sabon ƙawancen da aka kafa a ƙarƙashin ADC ya ba shi sabon fata game da makomar Nijeriya, yana mai cewa ko a lokacin ƙawancen da ya tallafa wa Buhari a 2014 da 2015, ba a samu irin wannan haɗin kai da tasiri ba. Ya ce wannan mataki ne na ceto Nijeriya daga hannun mutum guda da ke ƙoƙarin mallake ƙasar gaba ɗaya.
Momodu ya kuma sukar gwamnatin Tinubu, yana mai cewa Nijeriya ta ƙara taɓarɓarewa fiye da lokacin mulkin Buhari. Ya tambayi ‘yan Nijeriya ko halin da ake ciki a yau ya fi na shekaru biyu da suka wuce, yana mai cewa gwamnatin yanzu ta gaza wajen sauke nauyin da ke kanta. Ya bayyana ficewarsa daga PDP a matsayin wani mataki na neman sabuwar mafita ga ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp