Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Gombe ta kama wasu matasa 11 da ake zargi da Kalare tare da mallakar muggan makamai.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya miƙa wa LEADERSHIP Hausa.
- ‘Ƴansanda Sun Kama Mutane 12 Bisa Zarginsu Da Laifuka Daban-Daban A Gombe
- APC Ta Dakatar Da Sanata Bulus A Gombe Kan Zargin Yi Mata Zagon Kasa
Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin da cewa sun haɗa da: Abdullahi Saleh mai shekaru 18, da Yusuf Shitu mai shekaru 18, da Musa Saleh mai shekaru 20, sai Usman Suleiman mai shekaru 23.
Mahid Muazu yace sauran sune: Alhassan mai shekaru 19, da Aliyu Yakubu ɗan shekara 21, da Sadiq Adamu mai shekaru 21, sai Dauda Ibrahim da Haruna Mohammed mai shekara 18.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan ya ce, “A ranar 30 ga watan Mayun 2023, da misalin karfe 5:30 na yamma, al’ummomin anguwannin Pantami, da Malam-Inna, da Tudun-Wada da kuma Checheniya dake cikin garin Gombe, sun kai rahoto a ofishin Operation Hattara cewa wassu gungun matasa da ake zargin ƴan Kalare ne sun addabi anguwannin nasu da aika-aikar munanan laifuka”.
Yace samun wannan ƙorafi ke da wuya rundunar ta Operation Hattara ta kai farmaki maɓoyar ƴan Kalaren a wurare daban-daban, inda suka yi nasarar cafke waɗanda ake zargin.
ASP Mahid Abubakar ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Ya ƙara da cewa, “Makaman da muka kwato sun haɗa da adduna guda bakwai da wuƙaƙe guda uku”.
ASP Mahid Mu’azu ya yi ƙira ga al’ummar jihar su riƙa haɗa kai da ƴan sanda a ko da yaushe don inganta tsaron lafiyarsu ta hanyar bada bayanai masu amfani ga jami’an tsaro game da duk wani motsin da basu gamsu da shi ba.
Ya ƙara da cewa al’ummar jihar suna iya ƙiran lambobin gaggawa don kai rahoton duk wata matsalar tsaro a jihar. Yace lambobin su ne: 08150567771 ko 09165472923.