Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya damuwa da maganganun ‘yan siyasar Arewa da ke ayyana niyyar ƙalubalantar shi a zaɓen 2027, duba da yadda yankin Arewa ya kasa dunkulewa wuri guda.
Jibrin, wanda ke wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji ta jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka a shirin Politics Today na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Laraba. Ya ce, “Abin da muka saba yi shi ne, idan wani ya taso daga Arewa, sai mu haɗu mu rusa shi. Wannan shi ake yi. Kuma ina tabbatar maka, waɗanda suke cewa za su tsaya takara su kayar da Bola Tinubu, shi kuwa yana murna ne saboda yana ganin yadda muke cikin rikici da rarrabuwar kai.”
- Gwamna Yusuf Zai Kaddamar Da Majalisar Shurah Ta Jihar Kano
- Tinubu Ya Naɗa Shugabannin Jami’o’in Ilimi Na Tarayya Da Ke Zariya Da Kano
Ya tunatar da yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya samu saɓani da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, sakamakon adawar da wasu ƴan Arewa suka yi masa wajen neman ƙarfafa tushen siyasa. Haka kuma ya ambaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo da mai ci yanzu, Kashim Shettima, da su ma suka taɓa fuskantar irin wannan matsin lamba daga yankin Arewa.
Jibrin ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da shirye-shiryen siyasa suka fara ɗaukar zafi kafin 2027, inda batun rabon mulki (zoning) da neman haɗin kai ke ci gaba da jan hankali a fafutukar neman shugabanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp