• English
  • Business News
Saturday, September 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Ta’adda Sun Kashe Matafiya 12 A Filato 

by Abubakar Sulaiman
3 months ago
in Manyan Labarai
0
Ƴan Ta’adda Sun Kashe Matafiya 12 A Filato 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ƙalla matafiya 12 daga Zaria, jihar Kaduna aka kashe su a harin da ‘yan ta’adda suka kai a Mangu, jihar Filato a ƙarshen mako. Harin ya faru ne da ƙarfe 8 na dare ranar Juma’a lokacin da matafiyan ke kan hanyar zuwa ƙaramar hukumar Qua’an Pan domin halartar bikin aure.  

An bayyana cewa sama da matafiya 18 ne suke cikin babbar motar bas ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria a lokacin harin. Direban bas, wanda ma’aikacin ABU ne, shi ma ya mutu a harin, yayin da wasu suka samu munanan raunuka, tuni an kai su asibiti.

  • Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Filato, Mutane 15 Sun Mutu A Bokkos Da Mangu
  • EFCC Ta Kama Tsohon Kakakin Majalisar Filato Da Wasu ‘Yan Majalisa 14 Bisa Zargin Almundahana

Sheikh Suleiman Haruna, Imam na JIBWIS Mangu, ya tabbatar da cewa an ajiye gawarwakin takwas a babban Asibitin Mangu, yayin da ake neman sauran gawarwakin huɗu. “Jami’an tsaro sun duƙufa don gano waɗanda suka aikata wannan ta’asar,” in ji Imam.

Wanda ya tsira daga harin, Ibrahim Umar, ya ba da labarin cewa ‘yan ta’addan sun fara kashe direba, sannan suka kai hari ga sauran fasinjoji tare da kona motar. “Mun tsaya don yin tambaya ayi mana kwatance, amma ba zato ba tsammani suka kewaye mu suka fara kashe-kashe,” in ji Umar.

DSP Alfred Alabo, kakakin ‘Ƴansandan Filato, sun samu labarin faruwar lamarin kuma ana ci gaba da bincike. “Za mu fitar da cikakken bayani bayan an gama binciken,” in ji Alabo.

Labarai Masu Nasaba

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AttackFilato
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya

Next Post

Bam Ya Fashe A Kano, Ya Kashe Mutane 5

Related

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?
Manyan Labarai

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

8 hours ago
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

8 hours ago
Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban
Manyan Labarai

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

19 hours ago
Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi
Manyan Labarai

Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi

20 hours ago
NNPP
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025

1 day ago
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna
Manyan Labarai

Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato

1 day ago
Next Post
Bam Ya Fashe A Kano, Ya Kashe Mutane 5

Bam Ya Fashe A Kano, Ya Kashe Mutane 5

LABARAI MASU NASABA

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

September 19, 2025
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

September 19, 2025
An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

September 19, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

September 19, 2025
Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

September 19, 2025
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

September 19, 2025
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

September 19, 2025
Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

September 19, 2025
Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

September 19, 2025
Filato

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

September 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.