An tabbatar da cewa ’yan Boko Haram/ISWAP sun yi garkuwa da mata manoma 13 a yankin Askira-Uba, jihar Borno. Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Abdullahi Askira, ne ya tabbatar da lamarin, wanda ya faru ranar Asabar lokacin da wasu mata suka tafi yankin Mussa domin girbar amfanin gona.
Rahotanni sun nuna cewa yankunan Huyim da Mussa duk suna cikin karamar hukumar Askira-Uba, amma saboda rashin tsaro a Huyim, mata manoman sun koma Mussa da ake ganin ya fi kwanciyar hankali don samun abin dogaro da kai ta hanyar aikin gona. Askira ya ce ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ta tsere ta kuma koma gida, amma sauran ’yan matan masu shekaru 15 zuwa 20 suna hannun ’yan ta’addan.
- Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170
- ISWAP Ta Kashe Jami’ai 8 A Wani Sabon Hari A Borno
Dan Majalisar Dokokin Jihar Borno da Sanata Mohammed Ali Ndume sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara jajircewa wajen ceto waɗanda aka sace cikin gaggawa. Haka kuma sun bukaci al’umma su ci gaba da addu’a da bayar da cikakken goyon baya ga jami’an tsaro ta hanyar bayyana duk wani motsi ko zargin kai hare-haren ’yan ta’adda a yankunansu.
A cewar jami’an tsaro, ana cigaba da kokarin gano inda ake tsare da matan tare da tabbatar da komawarsu cikin aminci ga iyalansu.














