Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta fara gudanar da sintirin dare a ranar Talata domin aiwatar da haramcin ɗaukar fasinja da babura da kuma taƙaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe a wasu sassan jihar.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa rundunar ta taɓa jaddada cewa za ta sanya wa waɗannan dokoki hannu ne sakamakon sake tashin ayyukan ƴan fashi da ta’addanci da kuma yawaitar shigowar masu aikin babur a jihar.
Ayyukan sintirin, tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Hanyoyi da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Kano (KAROTA), na daga cikin sabon yunƙurin ƙarfafa tsaro da daƙile laifuka.
- Za A Rataye Mutane 2 Sakamakon Kashe Dan Acaba A Adamawa
- Hukuma Ta Gargaɗi Jama’a Kan Amfani Da Wuta A Lokacin Hunturu A Kano
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda ta jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Sai dai Kiyawa bai bayyana adadin ainihin motocin da aka kama ba, haka kuma bai fayyace ko haramcin ya shafi baburan da ake amfani da su na kai-tsaye na haya ba.
Daga baya ya bayyana cewa za a miƙa motocin da aka kama zuwa kotu domin ɗaukar matakin da ya dace.
Amma wannan matakin ya haifar da damuwa a tsakanin wasu mazauna jihar kan zargin kamun mutane ba tare da tantancewa ba.
Wani shahararren lauya mai kare haƙƙin ɗan’Adam da ke Kano, Abba Hikima, ya tunatar da ƴansanda cewa dokar 2013 da ta haramta ɗaukar fasinjoji da babur ta shafi masu sana’ar achaba ne kawai.
Ya ce: “Ina ta karɓar koke-koke cewa jami’an tsaro na kama mutanen kirki kawai saboda sun ɗauki fasinja, ba don kasuwanci ba.
Dokar 2013 da ta haramta ɗaukar fasinjoji da babur ta shafi masu ɗaukar fasinja don kasuwanci ne kaɗai, kuma hakane ainihin abin da ke haifar da barazana ga tsaro. A girmama haƙƙin jama’a,” in ji shi a shafinsa na Facebook.
Mazauna yankin sun yi kira ga ’yansanda da su bambanta a fili tsakanin amfani da babura na haya da kuma na masu zaman kansu, domin kauce wa take haƙƙin jama’a, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin magance matsalolin tsaro a jihar.














