ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani  

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
7 months ago
Annabi

… Ci gaba daga makon da ya gabata.

 Mu tafi a cewa, duk aya Uku, mu’ujiza ce, akwai ayoyi fiye da 6,000 a Alƙur’ani, in muka raba 6,000+ gida uku, za mu samu mu’ujiza 2,000+ acikin Alƙur’ani.

Annabi Musa AS, Ubangiji ya ambace shi da cewa, ya ba shi mu’ujiza 9 amma Annabi SAW, a Alƙur’ani mun samu 2,000+. Don haka, ba sai an yi tawili ba, a fili yake, Annabi SAW ya fi duk sauran Annabawan Allah. Sannan kuma, duk mu’ujizozin sauran Annabawa, zamani na tsawo suna kara shuɗewa, amma na Annabi SAW zamani na tsawo suna ƙara bayyana.

ADVERTISEMENT
  • Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani
  • Haaland Ya Kafa Sabon Tarihin Jefa Ƙwallaye A Gasar Firimiya

7 – Mu’ujizozin Annabi SAW sun fi na duk sauran Annabawa:

Yazo cewa, Alƙur’ani acikin sauran littattafai, kamar Annabi Adam (AS) acikin ‘ya’yansa. Da wannan za mu tabbatar cewa, Annabi SAW ya fi duk sauran Annabawa, saboda girman Annabi, itace girman mu’ujizarsa, kuma ya fi su duka.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

8 – Mu’ujizar Annabi SAW – Alƙur’ani: da yawa suna cewa, wai kar a yi fito-na-fito da Alƙur’ani saboda yana da fannoni da yawa, a’a, ai shi yafi cancanta a yi fito-na-fito da shi, saboda shi ne Mu’ujizarsa SAW, amma in kaɗauki wani abu wanda wataƙila bai inganta ba a matsayin hujja, sai a kunyata amma Alƙur’ani sai dai in baka fahimce shi ba.

Alƙur’ani harufa ne aka harhaɗa, aka iya karantawa kamar sauti, kamata ya yi a ce wannan shi ne zai ƙare, wata rana a nema a rasa amma abin mamaki, mu’ujizozin sauran Annabawa da suke da jini da ƙashi (Sanda, Raƙumi,…), sai ga su sun ƙare, an neme su an rasa, ko a gidan tarihi babu. Duk lokacin da aka nemi Alƙur’ani aka rasa, to duniyar ma a yi bankwana da ita.

Don haka, yana daga cikin mu’ujizar Alƙur’ani, abin da aka haddace shi ya fi tabbata daga abin da aka rubuta, duk da cewa, “abin da aka haddace, guduwa ya ke, amma abin da aka rubuta, tabbatacce ne.”

9 – Alƙur’ani ya faɗa mana duk halayen Annabawa (fa bi hudahum iƙtadih… ka yi koyi da shiriyarsu). Annabawa dukkansu, kowa yana da irin halin shi. Akwai “Halim”, “Shakur”,… kowanne da irin shiriyar da aka ba shi, ƙalla ka samu wanda aka haɗa masa biyu amma Annabi SAW, ce masa aka yi, “ya yi koyi da duka shiriyarsu an haɗa masa gaba ɗaya.

Wannan na nufin, ya yi koyi da su acikin kyawawan halayensu ba a Shari’arsu ba, saboda ta shi, ta shafe ta su.

Akwai Annabawa 124,000 a duniya, yanzu ana umartar Annabi SAW ya yi koyi da duka ɗabi’un wannan Annabawan, a lissafe ana nufin 1:124,000 ko kuma an ba shi zaɓi ya ɗauki kyawawan ɗabi’un na duka Annabawan.

 Don haka, Annabi SAW yake cewa, “an turo ni, in cika kyawawan ɗabi’u”. Ma’ana ba a ce babu ba amma an zo don a cika su. To tun da Annabi SAW ya cika su, to waye zai zo da wani abu sabo? Babu amma Allah zai iya taso da wani bawan Allah ya fayyace wannan kyawawan ɗabi’un na Annabi SAW wanda ba a fahimta sosai ba. Ma’ana wanda muka jahilta, sai wannan bawan Allahn ya bayyana mana ita. 

 A nan Shehu Ibrahim Inyass Kaulaka ke cewa, hatta littafi an gama rubutawa. Meye ma’anar rubuta littafi? Shi ne zuwa da wani sabon abu don bayyanawa mutane wani abun da basu sani ba, ko kuma warware musu wata matsala da ta dame su.

Wannan ya nuna mana cewa, Annabi SAW ya tattare ɗabi’un Annabawa 124,000 duka, don haka, a fili yake, Annabi SAW ya fi su duka.

10 – An aiko Annabi SAW ga duk halitta: (wama arsalnaka illa kaffatan linnasi bashiran wa nazira – ba a aiko ka ba, sai ga mutane baki ɗayansu, don ka zama mai bushara da gargaɗi a gare su). Duba da cewa, an aiko shi ne ga mutane baki ɗaya, don haka aikinshi zai fi yawa akan sauran Annabawa, hakan zai nuna cewa, ladanshi zai fi na su.

Idan za a ce, ga wani mutum shi kaɗai, ba shi da ƴan rakiya, ba shi da kuɗi, ba shi da kowa kuma ba shi da komai sannan ya ce wa duk duniya, ya ku Kafirai duk ku sauka akan tunaninku da addininku ku bi ni, wannan zai haifar da ƙiyayyar duniya ga mutumin nan. Abin da ya faru da Annabi SAW ke nan, sai da ya zama kowa maƙiyinshi ne sai wanda ya musulunta. Duk abin da ya faɗa wa mutanen wani gari, suka bijire, har ta kai ga ya yi Hijira, to duk inda aka koma, abin da aka faɗa wa mutanen garin da aka baro, su ma nan shi za a faɗa musu. Wannan ya nuna babu wurin guduwa kuma babu hutu. Misali, Annabin Kaduna, in ta yi zafi, sai ya koma Kano, amma in na Arewa baki ɗaya ne, sai ya koma Kudu, idan kuma na Nijeriya ne, sai ya tsallaka ƙasashen maƙwabta, in kuma na Afirka ne, ya yi wata nahiya, in kuma na duniya ne, shi kenan babu wurin gudu. Annabi kuwa SAW, Annabtarsa da duk mutanen cikin duniya ne.

Annabi Musa, wurin bani Isra’ila da Fir’auna kawai aka turo shi, don haka, da Misra ta yi zafi, sai ya tafi Falasɗin.

Kowane Annabi wurin wasu ƴan tsirarun mutane ake tura shi amma Annabi SAW ga duk duniya.

11 – Addinin Annabi Muhammad SAW,  shi ne mafificin addini, don haka wanda ya zo da Addinin, ya fi duk sauran Annabawan da suka zo da Addinai. Bugu da ƙari, Addinin Annabi SAW ya soke na sauran Annabawan mai wuya.

Duk abin da aka ce, na wasu ne banda wasu, za ka same shi mai wuya, amma abu na kowa da kowa, za ka same shi mai sauƙi. Don haka addinin Annabi SAW mai sauƙi ne, shi yasa ya zama na kowa.

Lallai wasu Malamai sun mayar da shi mai wuya, sai ya zama na wasu ƴan tsiraru amma wannan fahimtar su ce.

12 – Annabi SAW, shi ne mafificin al’umma duka: ta ina aka samo cewa, al’ummar Annabi SAW, itace mafificiyar al’umma, duk da cewa, magabatanmu sun fi mu yawan ibada, yawan shekaru da komai ma? Saboda Annabin wannan al’umma ya fi Annabawan sauran al’ummar da ta gabata. Ubangiji ya tabbatar da haka a Alƙur’ani da cewa, (Kuntum kaira ummatin ukrijat linnasi… – kun kasance mafificiyar al’umma a doron ƙasa…). Tun da al’ummar Annabi SAW ta zama mafificiya, me zai hana Annabinta ya zama mafificin halitta?

Wata rana, Annabi SAW ya ga Sayyadina Ali ya taho, sai yace masa, lale da shugaban Larabawa, Sayyada A’isha na zaune sai tace, ba kai ne shugaban Larabawa ba, sai yace, ni shugaban halitta ne baki ɗaya ba Larabawa kaɗai ba.

Annabi SAW ya iya kowane irin yare, in ka ganshi a barci, yarenka zai yi maka.

13 – Annabi SAW shi ne cika makon Ma’aika:Don haka ya zama shugaban su. Babu yadda za a yi, cika mako ya zamanto akwai wanda ya fi shi, ma’ana bai cika ba kenan. Ya zama cika mako ne don yana shugaban su.

14 – Fifiko tsakanin Annabawa ya danganta ne da wasu abubuwa kamar haka:

–  Yawan Mu’ujizozi: wanda ya fi yawan mu’ujiza ya fi girman daraja. Mu’ujiza tana nuna gaskiyar Annabi a bisa isar da saƙonsa. Mu’ujizar Annabi a Alƙur’ani kaɗai, ta haura 2,000+, ina kuma sauran da ya nuna wa Sahabbansa.

Annabi
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Next Post
GORON JUMA’A 05/12/2025

GORON JUMA'A 05/12/2025

LABARAI MASU NASABA

Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.