Rundunar Ƴansanda ta jihar Katsina ta kama mutane 64 tare da gano buhunan takin zamani 693 bayan zanga-zangar lumana da ta rikiɗe zuwa ta tashin hankali a jihar.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Ƴansandan ta jihar, Sadiq Aliyu, ya ce babu wanda ya rasa ransa, amma wasu ɓata gari sun lalata rumbun ajiya na gwamnati dake ɗauke da takin zamani a lokacin zanga-zangar.
- Mangal Ya Dauki Nauyin Yi Wa Masu Ciwon Mafitsara 80 Aiki A Katsina
- Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Rabon Shinkafar Da Tinubu Ya Bayar
Aliyu ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano dalilan da suka haifar da lamarin. Kama mutanen da kuma gano takin zamanin na daga cikin matakan da ake dauka don magance ɓarnar da aka yi.
Muƙaddashin gwamnan jihar, Faruq Lawal, ya ayyana dokar hana fita da kuma haramta yin zanga-zanga, wanda ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya a jihar.
An tura jami’an tsaro zuwa sassa daban-daban na jihar Katsina don tabbatar da bin dokar hana fita.