Rundunar ƴansanda ta babban birnin tarayya Abuja (FCT) ta cafke mutane huɗu, ciki har da ’yan mata biyu ’yan uwa, bisa zargin ƙulla garkuwa da kai na bogi domin karɓar Naira miliyan 5 daga hannun mahaifinsu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh, ta bayyana a yau Talata cewa lamarin ya faru ne a Jikwoyi, inda suka ƙaryar garkuwa da ɗaya daga cikin ’yan uwan don karɓar kuɗi daga mahaifinsu, Mista Innocent.
- Rikicin Makiyaya Da Manoma: An Kashe Mutum Daya, Gidaje 31 Sun Kone A Abuja
- Nijeriya Ta Gabatar Da Ƙudurin Karɓar Gasar Formula 1 A Abuja
An gano cewa ɗiyar mai shekara 16 ta bar gida ranar 18 ga Yuli domin rubuta jarabawa a makarantar Government Secondary School, Karu, amma bata dawo ba. Mahaifin ya samu kiran neman fansa daga wasu da ba a san ko su waye ba. Bayan haka, binciken sirri ta amfani da na’urorin zamani da ‘yansanda suka yi ya gano cewa yarinyar na zaune lafiya da sauran mutane a Jikwoyi Phase II, cikin annashuwa.
Bincike ya gano cewa babbar ‘yar gidan tare da saurayinta ne suka tsara shirin garkuwar, yayin da ƙaramar ‘yar ta amince ta shiga cikin lamarin. Saurayin kuma an bayyana cewa yana da aure. Babbar ‘yar gidan ta cigaba da zaune a gida tana kallon yadda iyayensu ke cikin tashin hankali suna yunƙurin tara kuɗin fansa.
Yanzu haka, ana tsare da dukkan mutanen hudu a hannun ’yansanda kuma sun amsa laifinsu. Rundunar ta ce za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike. Kwamishinan ‘yansanda na FCT, CP Ajao Adewale, ya soki wannan mummunan hali na cin amanar iyaye, yana mai shawartar iyaye su kula da tarbiyyar da yanayin rayuwar ’ya’yansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp