An sake cafke fitaccen mai fafutukar siyasa, Omoyele Sowore, bayan wata Kotun Majistare da ke Kuje ta ba shi beli a yau Juma’a, bayan tsare shi saboda zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴansanda sun sake kama Sowore daidai lokacin da ya fito daga kotu, inda ake sa ran za a gurfanar da shi a gaban babbar Kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, bisa wata sabuwar tuhumar daban.
- Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya
- Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
An dai kama Sowore ne a ranar Alhamis a harabar babbar Kotun tarayya bayan ya gana da jagoran ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu. Daga nan aka tafi da shi ofishin ƴansanda na babban birnin tarayya (FCT Command), inda aka tsare shi har zuwa safiyar Juma’a.
Ƴansanda sun ce Sowore ya karya doka ta kotu da ta hana ayarin gudanar da zanga-zanga a yankin Three-Arm Zone na Abuja. Sowore tare da lauya Aloy Ejimakor, ɗan’uwan Kanu, da wasu mutum 11 sun shiga hannun jami’an tsaro a ranar 20 ga Oktoba yayin zanga-zangar neman sakin Nnamdi Kanu.
Duk da haka, Kotun Majistare ta bayar da belinsu a ranar Juma’a, sai dai an sake kama Sowore nan take, abin da ke nuna cewa gwamnati na shirin gurfanar da shi bisa wasu sabbin tuhume-tuhume. Idan ba’a sake shi yau ba, hakan na nufin zai yi hutun ƙarshen mako a tsare kenan.













