Ɗaliban Kwalejin Kimiyya da Fasahar Lafiya da ke Jega a Jihar Kebbi, sun gudanar da zanga-zanga don nuna takaicinsu kan zargin hukumomin kwalejin da karkatar da Naira Miliyan 23, da suka ƙarba daga ɗalibai 250 na kammala karatu a kwalejin.
Zanga-zangar dai ta munana wadda ta kai ga fusatattun ɗaliban sun ƙona gidan shugaban ƙwalejin (Provost) Alhaji Haruna Saidu-Sauwa tare da lalata motoci.
- Xi Ya Amsa Wasikar Wakilan Daliban Da Suka Halarci Gasar Kere-Keren Kimiyya Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin
- Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Nijeriya Da ‘Yan Kwadago Sun Tashi Taro Babu Matsaya
Kamar yadda wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta ta bayyana, matsalar ta samo asali ne daga wani sabon sashen karatu da aka buɗe don kula da lafiyar al’umma wato (Public Health), inda hukumar kwalejin ta haɗa sashen karatu biyu guri daya da na Kiwon Lafiyar Muhalli don samun takaddun shaida Kammala karatu.
Dalilin hakan aka buƙaci ɗaliban su biya Naira 65,000 domin yin rajistar ma’auni, baya ga Naira 30,000 na farko da suka biya, inda ɗaliban suka hakan a matsayin hanyar karbar kudadensu tare da mayar da martani da kakkausar murya wanda ya kai ga zanga-zangar da sauran ta’adin da suka yi.
Tuni dai Ma’aikatan kwalejin sun gudu a cikin tsoro don guje wa fushin ɗaliban kafin isowar jami’an tsaro, inda Jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan Kebbi, SP Nafiu Abubakar, bayan tuntubarsa ya ce bai samu cikakken bayanin game da lamarin ba, amma da zarar ya samu sahihin bayani daga jami’in da ke kula da yankin zai bayar da ba’asi.