Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal a majalisar wakilai, Honarabul Abdussamad Dasuki, ya ƙaddamar da shirin karfafawa mata da Naira miliyan 10 a Sakkwato.
Shirin na masu ƙananan sana’oi na da manufar bunƙasa ɗorewar sana’o’in da mata suke a kai wanda mata 400 suka amfana da Naira dubu 25, 000 kowace a shirin mataki na farko.
- Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima…
- An ‘Yi Mummunar Arangama Da ‘Yan Bindiga A Sakkwato
A yayin da take ƙaddamar da shirin a Dogondaji a ranar Lahadi, uwar gidan dan majalisar, Hajiya Jamila Wada- Dasuki ta bayyana cewar an assasa shirin ne da zummar bunƙasa ƙananan sana’o’i a mazabar Kebbe/Tambuwal.
Ta ce an zabo waɗanda suka amfana ne a mazabu 11 da ke a Tambuwal da mazabu 10 da ke a Kebbe waɗanda dama masu gudanar da kananan sana’o’i ne wadanda suka hada da dinkin tela, saka, kiyon Awaki, fura da nono, tuyar kosai, noma da sauran su.
Hajiya Jamila ta bayyana cewar abin da matan ke yi muhimmi ne kuma abin yabawa, domin sun riga sun yi nisa a kasuwancin su wanda karfafa masu zai yi matukar tasiri a cikin al’umma.
A yayin da ta bayyana cewar a shiri na gaba za a zakulo matan karkara sosai ta ce ta jagoranci shirin ne ba wai a matsayin kashin kan ta ba, sai dai domin ta karfafawa mutum mai kishin al’umma da hangen nesan inganta rayuwar su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp