Jim kaɗan bayan gudanar da Sallar jana’izar marigayi Sarkin Kudun Gatawa, Isa Muhammad Bawa ba tare da gawa ba wanda da ‘yan ta’adda suka yi wa kisan gilla, ɗan sa wanda aka kama su tare ya bayyana ɗan siyasar da ya ba wa ƴan ta’addan kwangilar yin garkuwa da Sarkin.
Ɗan Sarkin, Kabiru Isa wanda ‘yan ta’addan suka saki a daren jiya bayan biyan kudin fansar miliyan 60 da babura biyar ba tare da bayar da gawar basaraken ba, ya bayyana cewar Honarabul Aminu Boza ne ke da hannu wajen garkuwa da basaraken.
- Ɗan Sarkin Gobir Da Aka Kashe Ya Kuɓuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Sayar da Tireloli 300 Na Shinkafa A Farashi Mai Rahusa
An gudanar da Sallar jana’izar basaraken na Daular Gobir a safiyar yau a Kanwuri da ke Sabon- Birni a inda dubban al’umma suka halarta cike da jimami da bakin cikin kisan gillar da aka yi masa.
A wani bidiyon da aka ɗauke shi kan gadon asibiti na daƙiƙu 30, Kabiru wanda shi ne ke tuka Sarkin a mota yayin da aka kama su ya ce Honarabul Aminu Boza ne ‘yan ta’addan suka ce masu ya bayar da Naira miliyan biyar a kama Sarkin. Ya ce da shi da Sarkin duk sun bayyana masu hakan tare da cewar sun ce a ɗora masa tara.
Honarabul Aminu Boza shi ne Ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Sabon-Birni ta Arewa a majalisa dokokin Jihar Sakkwato a jam’iyyar APC ya kuma yi fice a baya wajen shiga kafafen yaɗa labarai yana suka da caccakar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal da ta gabata kan abin da ya kira kasawarta wajen kawar da matsalolin tsaro a Sabon- Birni da Gabacin Sakkwato baki ɗaya.
Dan majalisar wanda daga baya ya canza sheka daga PDP zuwa APC, ba a taba jin ya shiga kafafen yaɗa labarai ya soki gwamnatin Ahmed Aliyu kan ta’addancin da ‘yan bindigar ke yi ba kamar yadda ya yi a baya ba duk kuwa da ta’azzara da lamarin ya ƙara yi a yanzu.