ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

τ-Law Ya Nuna Jajircewar Kasar Sin

by Sulaiman
3 months ago
filter: 0; fileterIntensity: 0.0; filterMask: 0; brp_mask:0;
brp_del_th:null;
brp_del_sen:null;
delta:null;
module: photo;hw-remosaic: false;touch: (-1.0, -1.0);sceneMode: 2621440;cct_value: 0;AI_Scene: (-1, -1);aec_lux: 0.0;aec_lux_index: 0;albedo:  ;confidence:  ;motionLevel: -1;weatherinfo: null;temperature: 39;

filter: 0; fileterIntensity: 0.0; filterMask: 0; brp_mask:0; brp_del_th:null; brp_del_sen:null; delta:null; module: photo;hw-remosaic: false;touch: (-1.0, -1.0);sceneMode: 2621440;cct_value: 0;AI_Scene: (-1, -1);aec_lux: 0.0;aec_lux_index: 0;albedo: ;confidence: ;motionLevel: -1;weatherinfo: null;temperature: 39;

A kwanan nan, kamfanin kimiyya da fasaha na kasar Sin Huawei ya sanar da τ-Law, wata ka’idar da ta shafi makomar sha’anin abubuwan hada kayan laturoni na “Semiconductor”, lamarin da ya girgiza kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha, da masu zuba jari na kasashe daban daban.To amma da farko me ake nufi da τ-Law? Bisa ilimin da ya shafi laturoni, τ alama ce mai bayyana tsawon lokacin da ake bukata wajen sauya bayanin sadarwa.

Idan τ ya ragu, sassan na’urorin laturoni na Chips za su zama masu karin inganci. A baya, ka’idar Moore’s Law ta yi shekaru fiye da 50 tana shawo kan bangaren kirkira da samar da na’urorin Chips, wadda ta jaddada bukatar kankanta sassan hada Chips da ake kira Transister a-kai-a-kai, a kokarin inganta na’urorin Chips din. Sai dai wannan ka’ida na fuskantar wuyar ci gaba da kankantar na’ura, da karuwar kudin da ake kashewa wajen gudanar da aikin, matsalolin da suka raunana makomar sha’anin hada Chips.

Abun farin ciki shi ne sabuwar ka’idar da kamfanin kasar Sin ya gabatar a wannan karo, za ta taimaka wajen daidaita matsalolin. Ta hanyar rage τ, wato takaita lokacin da ake bukata wajen sauya bayanin sadarwa, za a samu damar inganta Chips ba tare da kankanta na’urorin Transister dake cikin Chips din sosai ba. Kana yadda kamfanin Huawei ya yi nasarar kirkira, da samar da na’urorin Chips nau’ika 381 a baya, bisa ka’idar τ-Law, ya tabbatar da gaskiyar ka’idar, da makomarta ta fuskar kasuwanci.Kazalika, wani abin mamaki shi ne, dalilin da ya sa kamfanin Huawei ya iya gabatar da ka’idar τ-Law a wannan karo, shi ne takunkumin da kasashen yamma suka kakaba masa, bisa yunkurinsu na hana kasar Sin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha.

ADVERTISEMENT

Sakamakon yadda kasar Amurka da wasu kasashen Turai suka yi babakere a bangaren samar da Chips mafi ci gaba, da kuma yadda suka hana kamfanin Huawei samun Chips din, da injuna masu ruwa da tsaki, ya sa wajibi kamfanin Huawei ya yi kokarin daidaita tsare-tsaren Chips na kansa, inda ya samu nasara, tare da kare matsayinsa na kasancewa kan gaba a duniya, ta fuskar fasahar hada Chips, da sauran bangarori daban daban.

Hakan ya nuna jajircewar kasar Sin, inda yunkurin tare hanyarta ke sanya ta kara samun ci gaba.To, ko mene ne asalin jajircewar Sin? Amsa ita ce burin Sin na raya kanta, don zama wata kasa mai cikakken karfin kimiyya da fasaha, da kwarewar da kasar ta samu a fannonin masana’antu, da kula da al’umma, yayin da take kokarin cika wannan buri. Ban da haka, wani babban dalilin da ya sa ake samun wannan jajircewa shi ne halayyar Sinawa ta dogaro da kai, da iya jure wahala.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A shekaru fiye da 10 da suka wuce, mun gane ma idanunmu yadda kasar Sin ta kawar da shingayen da aka sanya mata, ta samu nasara wajen kirkiro dimbin sabbin fasahohi, da samar da kayayyaki masu farin jini a duniya. Kana sabuwar ka’idar τ-Law da aka gabatar a wannan karo ta sake shaida cewa, duk wata wahala, ba za ta taba hana kasar Sin samun ci gaba ba. (Bello Wang)

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Manchester Utd Za Ta Biya Amorim Yuro Miliyan 16 Sakamakon Korar Da Ta Yi Masa

Manchester Utd Za Ta Biya Amorim Yuro Miliyan 16 Sakamakon Korar Da Ta Yi Masa

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.