ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

by Sulaiman
23 minutes ago
Sin

Fasahar kirkirarriyar basira ta AI, da mutum-mutumin inji, da sauran fasahohin zamani suna kara yin tasiri ga rayuwarmu. A cikin wannan hali, me ya kamata ‘yan Afirka su yi? Shin ya kamata su nade hannu su jure duk wani tasirin da sabbin fasahohi suke haifarwa? Ko kuma su shiga ayyukan nazarin kimiyya da fasaha, da na kula da harkoki masu nasaba da sabbin fasahohi, da more ingantacciyar rayuwa da ci gaban fasahohi ya haifar? A kan wannan batu, kasar Sin har kullum tana fatan ganin kasashen Afirka sun dauki dabara ta biyu.

A yau Alhamis aka rufe taro kan Intanet na kasa da kasa na Wuzhen na bana, wanda ya gudana a birnin Wuzhen na kasar Sin. Wani sakamako na taron shi ne yadda aka fitar da “Shawarar Gina Tsarin Fasahar AI Mai Budadden Bayani A Duniya”. Wannan shawarar ta jaddada bukatar hadin gwiwar dukkan kasashe a harkokin da suka shafi fasahar AI, wadda ta nuna ra’ayin kasar Sin na bude kofa da neman amfanar da kowa, dangane da fasahar zamani ta AI.

Hausawa su kan ce “Kyan alkawari cikawa”. To, ta yaya kasar Sin ke cika alkawarinta a wannan fanni? Bari mu kalli yadda kasar ke amfani da tsarinta na gargadin yanayi mai amfani da fasahar AI, wato “Mazu”, wajen hidimtawa mutanen Afirka. A Djibouti, “Mazu” na iya fitar da gargadin yanayi mai tsanani, inda yake samar da kariya ga ayyukan tashar jiragen ruwa. A Habasha, ana amfani da tsarin “Mazu” wajen tinkarar ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa. Yayin da sauran kasashen Afirka, kamar su Najeriya, da Kamaru, da Guinea, da Kodibwa, su ma suke shirin kaddamar da tsarin “Mazu” a cikin gida.

ADVERTISEMENT

Kana wani abu mafi mahimmanci shi ne, hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka a wannan fanni yana da nufin ba su damar fitar da gargadin yanayi mai tsanani bisa karfinsu. Dangane da batun, sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, “Wannan shi ne ainihin tsarin hadin gwiwa da duniya ke bukata, wato a taimaka wa kasashe ta hanyar mika fasaha, da gudanar da bincike tare, da karfafa musu kwarewar aiki, ta yadda za su iya kare mutanensu.”

A nasu bangare, mutanen kasashen Afirka sun fahimci ra’ayin kasar Sin, kuma sun yaba da tasirin da kasar ke bayarwa kan batun tabbatar da daidaiton fasahar zamani a duniya. Kamar yadda jaridar kasar Namibia ta “Windhoek Observer” ta wallafa wata makala a kwanan baya, wadda ta yaba wa kasar Sin kan yadda take karbar bakuncin taro kan Intanet na kasa da kasa na Wuzhen a ko wace shekara, inda ake cewa, taron Wuzhen ya shafi makomar ayyukan yanar gizo ta Intanet, wato ko fasahar dijital za ta kasance karkashin mallakar wasu kamfanoni, ko kuma za a hada karfin bangarori daban daban na duniya, don raya fasahar, da more ta tare. (Bello Wang)

LABARAI MASU NASABA

Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

Li Qiang Ya Gana Da Darakta Janar Na Hukumar WIPO

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu
  • Sulaiman
    NNPC Ya Samu Koma Baya Bayan Tura N11.14tn Asusun Tarayya Cikin Watanni Tara
  • Sulaiman
    Yadda Tinubu Ke Yawan Ciyowa Nijeriya Bashi Abin Tambaya Ne – Atiku
  • Sulaiman
    Majalisa Ta Nemi Hukunta Asibitocin Da Suka Ƙi Karɓar Majinyatan Gaggawa

MASU ALAKA

Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane
Daga Birnin Sin

Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

November 4, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Darakta Janar Na Hukumar WIPO
Daga Birnin Sin

Li Qiang Ya Gana Da Darakta Janar Na Hukumar WIPO

November 4, 2026
Han Zheng Zai Tafi Turkiye Don Halartar Taron Kolin Kasashen Da Suka Daddale Yarjejeniyar Sauyin Yanayi Ta MDD
Daga Birnin Sin

Han Zheng Zai Tafi Turkiye Don Halartar Taron Kolin Kasashen Da Suka Daddale Yarjejeniyar Sauyin Yanayi Ta MDD

November 4, 2026

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

November 5, 2026
ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

APC Na Son Jefa Nijeriya Cikin Rikici – ADC

November 5, 2026
Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

Wane Tasiri Ƙarin Ciyo Bashin Dala Biliyan 7.7 Zai Yi A Kasafin Kuɗin Nijeriya Na Gaba?

November 5, 2026
Yadda Masu Amfani Da Moniepoint Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Na Gwamnatin Tarayya

Yadda Masu Amfani Da Moniepoint Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Na Gwamnatin Tarayya

November 5, 2026
Rikicin Siyasa: Shin ’Yan Takarar Jam’iyyun Adawa Suna Samun Tsaron Da Ya Dace A Yaƙin Neman Zaɓen 2027?

Rikicin Siyasa: Shin ’Yan Takarar Jam’iyyun Adawa Suna Samun Tsaron Da Ya Dace A Yaƙin Neman Zaɓen 2027?

November 5, 2026
Yadda Masu Amfani Da OPay Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Kyauta Daga Gwamnati

Yadda Masu Amfani Da OPay Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Kyauta Daga Gwamnati

November 5, 2026
Shirin Atiku Na Dawo Da Tallafin Mai Zai Dawo Da Nijeriya Baya Da Shekaru 20 — TSG

Atiku Ya Zargi APC Da Amfani Da Kotu Domin Raunana ADC

November 5, 2026
Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da ALAT By Wema Bank Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da MoMo PSB Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

November 5, 2026
Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da ALAT By Wema Bank Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da ALAT By Wema Bank Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

November 5, 2026
Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da Naira Gram Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da Naira Gram Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

November 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.