Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufa’i Alkali, a ranar Larabar, ya bayyana cewa jam’iyyar a shirye take ta hada kai da wasu Jam’iyyun siyasa kafin zaben 2023 mai zuwa.
Mista Alkali, mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ne kan harkokin siyasa, ya bayyana hakan a Legas a wani taron manema labarai.
- Rikicin NNPP: Kwankwaso Ya Ci Amanarmu – Shekarau
- Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba – Kwankwaso
A cewarsa, jam’iyyar ba ta kyamar tattaunawa don gina kasa.
“Jam’iyyun da ke son tattaunawa da jam’iyyar NNPP ba aibu ba ne su yi hakan a don samar da tafiya daya mai karfi, kuma dole ne mu bayyana ra’ayoyinmu kan makomar kasar nan.
“Dukkan jam’iyyu daidai suke a gaban doka.
“Muna magana ne game da makomar Nijeriya,” in ji Mista Alkali, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa.
Ya kuma yi tir da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a Nijeriya, yana mai cewa bai kamata mutane su zo a tattauna a fitar da dan takara daya tilo.
Tattaunawar kawance tsakanin jam’iyyun NNPP da Labour ta tsawon makonni ta gaza haifar da sakamako, shi ya sa ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun biyu – Mista Kwankwaso da Peter Obi – suka bayyana a matsayin ‘yan takara.
Alkali ya ce idan wata jam’iyya ta zauna don tattaunawa, dole ne su fara kokarin fahimtar kansu: mene ne suke da alaka da su – akida, hangen nesa, buri da kuma manufofin yin aiki tare.
Ya kara da cewa ya kamata jam’iyyu su amince da matakin kawance ko dai a majalisar wakilai, wakilai, dattijai, gwamna ko shugaban kasa.
“A siyasa muna magana ne game da kwazon aiki.”
Shugaban, ya ce Nijeriya ba za ta iya yin kuskure a 2023 ba, yana mai cewa jam’iyyar NNPP za ta bullo da sabbin dabarun gina tattalin arzikin kasa idan aka zabe shi.
Ya kara da cewa “NNPP tana wa Nijeriya shiri kuma za su kawo sauyi ga al’amuran siyasar kasar.”
Ya kara da cewa jam’iyyar NNPP ta kasance jam’iyyar siyasa mafi girma a Nijeriya kuma nan ba da dadewa ba za ta samu goyon bayan mafi yawan ‘yan Nijeriya a fadin kasar.
Ya ce jam’iyyar NNPP za ta ci gaba da bin ka’idojinta na inganta rayuwar talakawan Nijeriya.
“Abin da Nijeriya ke bukata shi ne shugabancin da mutane za su amince da su kuma za su samar,” in ji Alkali, farfesa a fannin kimiyyar siyasa da tattalin arziki.
Akan tikitin takarar musulmi da musulmi, shugaban ya ce hakkin dan takara ne ya zabi abokin takararsa, yana mai cewa abin da ya kamata ya fi dacewa shi ne tunkarar kalubalen Nijeriya.
Ya kara da cewa: “Idan muna son kasar nan ta canza dole ne mu wuce batun maganar yankin yanki da tattaunawa kan addini.
“Mun wuce matakin sabani na yanki da ra’ayin addini.” (NAN)