Kwanaki kadan da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu ta umarci jam’iyyar APC da ta mika sunan Bashir Shariff Machina a matsayin halartaccen dan takarar sanatan Yobe ta arewa.
Ahmed Lawan dai ya yi na’am da wannan hukunci wanda ya bayyana cewa bai zai daukaka kara ba.
- Yara 3 Sun Tsere Daga Maboyar ‘Yan Bindiga Yayin Da Suke Barci A Abuja
- Adron Homes Na Taya Nijeriya Murnar Cika Shekaru 62 Da Samun ‘Yancin Kai
Wannan hukuncin ne ya tabbatar Ahmed Lawan ba zai koma zauren majalisan dattijai ba. Inda tuni har gwamnoni masu ci da tsofafi sun far ahankorar kujerarsa. Akwai sama da gwamnoni 28 masu ci da kuma tsofaffi daga cikin jam’iyyar APC da PDP wadanda suke neman kujeran majalisar dattawa a mazabunsu.
A yayin da a arewa ake da tsofaffi gwamnoni da wadanda suke kan kujera 18, yayin da a yakin kudu kuwa akwai gwamnoni masu ci da tsofaffi 11 da suke neman wanna kujera. Tsofaffin gwamnoni da suka tsaya takarar kujerar majalisar dattawa a babban zaben shekara ta 2023 su ne; Adams Oshiomhole (Edo), Aliyu Wamakko (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Kabiru Gaya (Kano), Abubakar Bagudu (Kebbi), Chimaroke Nnamani (Inugu), Tanko Al-makura (Nasarawa), Danjuma Goje (Gombe), Simon Lalong(Filato), Gbenga Daniel (Ogun), Sani Bello (Neja), Samuel Ortom (Benuwe) da kuma Theodore Orji (Abiya).
Sauran sun hada da Ifeanyi Ugwuanyi (Inugu), Darius Ishaku (Taraba), Ibrahim Gaidam (Yobe), Seriake Dickson (Bayelsa), Okezie Ikpeazu (Abiya), Saminu Turaki (Jigawa), Gabriel Suswan (Benuwe), Ibrahim Shekarau (Kano), Dabe Umahi (Ebonyi), Adamu Aliero (Kebbi), Aminu Tambuwal (Sakkwato),Sam Egwu (Ebonyi), Ibrahim Dankwambo (Gombe), Godswill Akpabio (Akwa Ibom) da kuma Orji Kalu (Abiya).
A wannan majalisar da za ta kare ranar 11 gawatan Yunin 2023, akwai tsofaffin gwamnoni 14 da a yanzu haka suke zauren majalisar dattawa a matsayin sanatoci, da suke wakiltar mazabunsu mabambanta daga yankunan arewa da kudu.
A binciken da LEADERSHIP ta gudanar ta gano cewa wadanda suke kan gaba wajen neman wannan kujera na shugabancin majalisar dattawa su ne gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwalna jam’iyyar PDP da tsohon gwamnan Jihar Abiya, Orji Uzor Kalu wanda a yanzu haka shi ne mai tsawatarwa na majalisar dattawa.
Haka kuma akwai gwamnan Jihar Ebonyi, Dabe Umahi shi ma idonsa na kan wannan kujera duk da cewa wannan ne karonsa na farko a zauren majalisa. Kalu da Umahi dukkansu ‘yan jam’iyyar APC ne. LEADERSHIP ta gano cewa burin Tambuwal na zama shugaban majalisar dattawa na daya daga cikin dalilan da ya sanya ya janye takararsa ta shugaban kasa tare da mara wa Atiku Abubakar baya a lokacin da aka yi zaben fitar da ‘yan takara na shugaban kasa a jam’iyyar PDP a watan Mayu.
Baya ga wannan kuma, jaridar ta gano cewa wannan dalilin ne ma ya sanya aka ba shi daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP don ya yi iya bakin kokarinsa don ganin PDP ta samu nasara a zaben 2023.
Tambuwal dai ba sabon fuska ba ne a majalisar kasa. Tsohon shugaban majalisar wakilai kafin ya tsaya takarar gwamnan Jihar Sakkato wanda ya yi nasara. Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a lokacin da yake sukar jam’iyyar kan rashin ba shi takara, ya ce Tambuwal ya janye wa Atiku ne don yana hararar kujerar shugaban majalisa ne.
A cikin jam’iyyar APC, bayanai na nuna cewa dan majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan Jihar Abiya wanda a yanzu haka shi ne mai tsawatarwa a zauren majlisar, Orji Uzor Kalu ya nuna sha’awarsa na son zama shugaban majalisar dattawa.
An kuma gano cewa suna da kyakkyawar alaka da abota tsakaninsa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu. Kalu ya yi iya bakin kokarinsa wajen cusa Tinubu ya zama dan takaran shugaban kasa don yankin kudu maso gabas ya samu shugabancin majalisar dattawan.
Shi dai ya samu gogewa a majalisa ta tara don har mukami yake da shi. Gwamnan Jihar Ebonyi, Dabe Umahi shi mai donsa yana kan wannan kujera ta zama shugaban majalisar dattawa. Duk da yake ba shi da gogewa a zauren majalisar kasancewarsa wannan ne karonsa na farko a majalisar, dan jam’iyyar APC ne da ya fito daga yankin kudu maso gabashin Nijeriya.
Wani wanda ake kyautata zaton suna kan gaba wajen neman shugabancin majalisar dattawa a karo na 10 shi ne, Sanata Kabiru Gaya dan jam’iyyar APC daga Jihar Kano. Yana daya daga cikin ‘yan majalisa da suka dade a zauren majalisa. A daidai wannan lokaci, jam’iyyun siyasa da kungiyoyin kare hakkin fararen hula sun nuna kin amincewarsu kan yadda tsofaffin gwamnoni 28 da suke ‘yan takarar majalisar dattawa na APC da PDP.
Kungiyoyin kare hakkin fararen hular sun ce mafi yawan tsofaffin gwamnoni da suke tseren shiga zauren majalisar dattawa suna yi ne don kare kasuwancin da suke yi, su kuma jam’iyyun siyasa
suna sanya ‘yan takarar da suke tunanin samun wasu abubuwan da za su samu. Sun kara da cewa amma zabi ya rage ga ‘yan Nijeriya, su zabi wanda suke so.
Da yake tattaunawa da LEADERSHIP, shugaban hukumar hulda a tsakanin jam’iyyu (IPAC) karkashin inuwar dukkan jam’iyyun siyasar Nijeriya, Yabagi Sani ya bayyana cewa samar da ‘yan takara ba shi ne sakamakon zabe ba.
“Ba zan iya bayyana wanda ‘yan Nijeriya za su zaba ba. Kai-tsaye ba zan iya tursasa wa jam’iyyun siyasa kan wadanda za su tsayar taka ba. Wannan ya ta’allaka ne ga wadanda mutane suke so su zaba. Idan suka zabe su shi kenan.
“Idan ‘yan Nijeriya suka zabe su a matsayin ‘yan majalisar dattawa shi kenan. Sannan idan suka zabe su, to su kasance sun gudanar da aiki da ya rataya a wuyansu,” in ji shi. Sai dai kuma kungiyoyin sun koka kan tsofaffin gwamnoni guda 28 a jam’iyyu biyu da ke neman wannan kujera, inda suka ce idan suka samu nasarar lashe zabe, to za su iya zubar da kimar majalisar dattawa.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin fararen hulda da masu zaman kansu, Awwal Musa Rafsanjani ya bayyana cewa ganin yawan adadin tsofaffin gwamnoni da ke neman darewa kan kujerar majalisar dattawa, ba za su taba iya gudanar da aiki yadda ya kamata ba.
“Zauren majalisar dattawa ya zamar wa gwamnoni kamar wurin ritaya ne a gare su. Sun mayar da zauren majalisar kamar wurin da mutanen da ba su da amfani a cikin siysa.
“Ba ma tunanin tsofaffin gwamnoni su mamaye majalisar dattawa domin ba za a samu ci gaba ba. Suna bukatar matsayin ne domin karfafa siyasar su da ci gaba da samun kadadensu, amma ba domin gudanar da ayyukan majalisa ba.
“Mafi yawancinsu sun gaza a jihohinsu lokacin da suke rike da mukama gwamnoni, domin haka, zuwan su majalisa ba za su iya tabuka komai ba kamar yadda suka gaza a jihohinsu,” in ji Rafsanjani.
Ga dai jerin gwamnoni masu ci da tsofaffi da ke hankorar neman kujerar shugaban majalisar dattawa kamar haka:
Sam Egwu da kuma Dabe Umahi (Ebonyi)
Dakta Sam Egwu ya kasance farkon gwamnan Jihar Ebonyi na farar hula, wanda a yanzu haka yake neman takarar kujerar majalisar dattawa na yankin Ebonyi ta arewa karkashin tutar jam’iyyar PDP a karo na uku. Shi ma takwararsa, Cif Dabid Umahi wanda shi ne gwamnan jihar a yanzu, yana neman takarar kujerar majalisar dattawa ta yankin kudancin Ebonyi karkashin jam’iyyar APC.
Abdul’Aziz Yari (Zamfara)
Sakamakon sulhu tsakaninsa da gwamnanj ihar, Bello Matawallle, tsohon gwamna Jihar Zamfara, Abdul’Aziz Yari ya samu tikitin tsayawa takarar dan majalisar dattawa na yankin Zamfara ta yamma. Yari ya kasance shi kadai ne dan takarar kujerar majalisar dattawa a jam’iyyar APC na Zamfara ta yamma tun kafin gudanar da zaben fid da gwani. Yari ya kasance gwamnan Jihar Zamfara har karo biyu a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019.
Ya taba zama dan majalisar wakilai na tarayya. Ya yi takarar kujerar majalsar dattawa a shekarar 2019, ya ci zabe amma sai dai kotun koli ta soke nasarar jam’iyyar APC a Jihar Zamfara gaba daya.
Gbenga Daniel (Ogun)
Tsohon gwamnan Jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel shi ne dan takarar kujerar dan majalisar dattawa na yankin Ogun ta gabas a karkashin jam’iyyar APC. Daniel ya rike gwamnan jihar har karo biyu a tsakanin 2003 zuwa 2011, ya zama dan takarar jam’iyyar APC na yankin Ogun ta gabas a jam’iyyar APC lokacin da ya doke dan majalisa mai ci, Sanata L’ekan Mustapha.
Theodore Orji, Orji Kalu da kuma OkezieIkpeazu (Abiya)
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa lokacin da tsohon gwamnan Jihar Abiya kuma sanatan Abiya ta tsakiya, Sanata Theodore Orji Uzor ya bar jam’iyyar PDP bayan ya zama dan majalisa har sau biyu, ya ci gaba da neman mukami a majalisar zartarwa. A yanzu haka dai Orji Uzor Kalu yana neman ci gaba da zama dan majalisar dattawa na yankin Abiya ta arewa a karkashin jam’iyyar APC.
A daya bangaren kuma, takwaransa, Okezie Ikpeazu yana neman zama dan majalisar dattawa na yankin Abiya ta kudu, wanda suke jam’iyya daya, inda aka zabe shi a matsayin gwamna tun a shekarar 2015, yana neman wannan kujera ne a karshe nmulkinsa da zai kare a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Kalu ya kasance gwamna na farko a jihar a jamhuriya ta 4 tsakanin 1999 zuwa 2007 a karkashin jam’iyyar PDP, an kuma zabe shi a matsayin dan majalisar dattawa a shekarar 2019. Orji yana zauren majalisar ne tun a 2007 har zuwa yau.
Samuel Ortom da kuma Gabriel Suswam (Benuwe)
Sanata Gabriel Suswam ya kasance gwamnan Jihar Benuwe a tsakanin 2007 zuwa 2015, inda a yanzu haka yake matsayin dan majalisan dattawa mai wakiltar Benuwe ta arewa, sannan ya kasance tsohon dan majalisar wakilai na tarayya. Shi kuma gwamnan Jihar Benuwe na yanzu, Samuel Ortom yana neman zama dan majalisar dattawa a zaben 2023.
Ya tsaya takarar ne a yankinarewa maso yammacin Benuwe.
Adamu Aliero (Kebbi)
Sanata Mohammad Adamu Aliero ya kasance gwamnan Jihar Kebbi har sau biyu a tsakanin shekarar 1999 zuwa. Ya zama sanata a 2007 da yake wakiltar Kebbi ta tsakiya kafin daga bisani tsohon shugaban kasa Marigayi Umaru Musa Yar’Adu’a ya nada shi ministan Abuja. Bayan mutuwar shugaban Yar’Adua, ya dawo gida, inda ya yi takarar tare da lashe kujerar dan majalisar dattawa na yankin Kebbi ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP tsakanin 2011 zuwa 2019.
Simon Lalong (Filato)
Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong zai kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu a watan Mayun shekara mai zuwa. Gwamnan ya tsaya takarar majalisar dattawa a yankin Filato ta kudu karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Chimaroke Nnamani da Ifeanyi Ugwuanyi (Inugu)
Tsohon Gwamnan Jihar Inugu, Dakta Chimaraoke Nnamani an ba shi takarar kujerar dan majalisa dattawa na yanakin Inugu ta yamma a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023. Bayan ya kammala wa’adinsa har karo biyu a matsayin gwamnan Jihar Inugu a tsakanin 1999zuwa 2007, Nnamani ya lashe kujerar sanata a karkashin jam’iyyar PDP. Ya kasance sanata tun daga 2007 har zuwa 2011.Ya dai maye gurbin Sanata Gilbert Nnaji a cikin jam’iyyar PDP. Nnamani ya sake zama dan majalisar dattawa a 2019, zai sake zama sanata ne har karo hudu idan ya samu nasarar lashe zabe a 2023.
Haka kuma gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya tsaya takarar kujerar dan majalisar dattawa na yankin Inugu ta arewa.
Attahiru Bafarawa da Aliyu Wamakko da kuma Alhaji Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato)
Tsofaffin gwamnoni guda biyu na Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa da kuma Alhaji Aliyu Wamakko dukkansu na neman gurbi a zauren majalisar dattawa tare da gwamna mai ci, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.
Bafarawa ne kadai bai taba neman kujerar sanata ba, ya dai tsaya takarar shugaban kasa a 2017 karkashin jam’iyyar DPP. Wamakko da Tambuwal za su gwabza na neman kujerar takarar sanata na Sakkwato ta kudu a APC da kuma PDP.
Alhaji Aliyu Wamakko shi ne ya gaji Bafarawa bayan ya kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu, sannan zai kasance dan majalisar dattawa karo nau ku idan ya samu nasarar lashe zabe a 2023.
Danjuma Goje da Ibrahim Dankwambo (Gombe)
Sanata Danjuma Goje da ke wakiltar Gombe ta tsakiya, ya kasance gwamnan Jihar Gombe har karo biyu a tsakanin 2003 zuwa 2011. A yanzu haka yana matsayin satana ne karo na uku a zauren majalisar dattawa.
Ibrahim Dankwambo ya taba rike babban akanta na kasa karo guda, sannan ya kasance gwamnan Jihar Gombe a tsakanin 2011 zuwa 2019. Dankwambo yana takarar satana da shi da Sa’idu Alkali wanda ya kayar da 2019.
Sani Bello (Neja) A Jihar Neja, Gwamna Alhaji Abubakar SaniBello ya samu tikitin takarar sanata na yankin Nejat a arewa a karkashin jam’iyyar APC wanda ya kada Sanata Sabi Abdullahi.
Adams Oshiomhole (Edo)
Tsogon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole shi ne dan takarar sanata a yankin Edo ta arewa a karkashin jam’iyyar APC. Ya kasancetsohon shugaban APC na kasa kuma tsohon shugaban kungiyar kwadugo na kasa.
Tanko Al-Makura (Nasarawa)
Sanata Tanko Al-Makura ya kasance gwamnan Jihar Nasarawa a tsakanin 2011 zuwa 2019 karkashin jam’iyyar CPC wacce ta yi maja zuwa APC. Al-Makura yana neman zama dan majalisar dattawa na yankin Nasarawa ta kudu.
Saminu Turaki (Jigawa)
Sanata Ibrahim Saminu Turaki ya kasance gwamnan Jihar Jigawa a tsakanin 1999 zuwa 2007 karkashin rushasshiyar jam’iyyar ANPP. Haka kuma ya kasance sanata mai wakiltar Jigawa ta kudu maso yamma a tsakanin 2007 zuwa 2011 karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Ya sake shiga jam’iyyar PDP a 2019, inda ya tsaya takarar sanata amma ya fadi a hannun dan takarar jam’iyyar APC.
A yanzu haka dai shi ne dan takarar a jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa. Hari ila yau, a fagen siyasar Nijeriya yayin da ya rage kasa da watanni biyar a fara gudanar da babban zaben 2023, yawancin jam’iyyun siyasa sun kasa warware rikicin cikin gida.
Inda a cikin jam’iyyar PDP da har yanzu da sauran rina a kaba bayan da kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP suka gaza sulhunta tsakanindan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaj iAtiku Abubakar da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike.
A bangaren jam’iyyar APC kuwa, nan ma ba ta canza zani ba, domin kuwa gwamnonin jam’iyyar na ganin an yi watsi da su wajen fitar da kwamitin yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnonin jam’iyyar APC za su gana da daraktan janar na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, gwamna Jihar Filato, Simon Lalong domin warware takaddamar da ke tsakani.
Sai kuma sauran jam’iyyun kamar irin su LP, SDP, NNPP har yanzu ba su fitar da kwamitin yakin neman zaben su ba. Yayin da jam’iyya ADC take cikin rikicin gida dumu-dumu.