Manjo Hamza Al- Mustapha (mai ritaya) kuma tsohon dogarin marigayi shugaban kasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, ya yi gargadin cewa ana shigo da makamai da kwayoyi zuwa cikin kasar nan don a yi amfani da su a lokacin zaben 2023.
Al-Mustapha, wanda dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar Action Alliance, ya ce, ba sani ba ko ana shigo da makaman ne don a kara karfafa yakar ta’addanci ko kuma an shigo da su ne don wata manufa ta siyasa.
- Masari Ya Barke Da Kuka Yayin Gabatar Da Kasafin Kudinsa Na Karshe
- Matafiya 17 Da Suka Taso Daga Legas Zuwa Gombe Sun Kone Kurmus A Hadarin Mota
Dan takarar wanda ya sanar da hakan a wani taron tattaunawa da wata jaridar Platinum Post ta shirya, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan da suka dace domin aldakile shigo da makamai cikin kasar nan kafin a fara gudanar da zabukan 2023.
Ya da cewa “Ban san ko daukacin hukumomin tsaro a kasar nan, sufeto janar na ‘yansanda ko suna sane da abin da na ke son na fada a nan ba, a yanzu haka ana shigo da makamai da kwaya zuwa cikin kasar nan ta hanyar iyakokin kasar nan, ba na kuma jin ko al’umma na sane da wannan.
“Shin da umarnin wa ake shigo da makaman, me ya sa abin ke kara karuwa, su waye suka bukaci a shigo da su da sauransu?