Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, Babachir Lawal, ya ce zabin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahgmed Tinubu ya yi na Musulmi a matsayin mataimakinsa babban kuskure ne.
A ranar Lahadi ne Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.
- Da Dumi-Dumi: Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Sakamakon Rushewar Gini A Legas
- An Tsinci Gawar Jarumin Fina-Finan Nollywood, Abuchi Ikpo A Gidansa
Lawal, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Talata, inda ya ce daukar wannan matakin kuskure ne babba.
Tsohon sakataren gwamnatin wanda ya mara wa Tinubu baya a zaben fidda-gwanin APC, ya ce zaben na Shettima ya nuna cewa wasu ‘yan baranda kuma ‘yan amshin-shata ne suka takura Tinubun ya yi haka.
Ya ce bisa ga dukkan alamu, gwamnonin arewa da wasu manyan arewa ne suka sa hakan ta faru, inda ya ce ba za su taba zabar dan takarar da ke da mataimaki Kirista dan arewa ba, kuma shi Tinubun ya yarda da su, in ji Babachir.
Ya yi gargadi da cewa, ”Idan har Tinubun yana ganin wannan zabin shi zai ba shi nasarar samun kuri’un Musulmin arewa, to ya yi kuskure.”
”Saboda za su yi tururuwa su zabi daya daga cikin ‘ya’yansu ne, saboda haka al’adarsu take” In ji shi.
”Buhari, wanda shi ne dansu na fari ba zai kasance dan takara ba a 2023. Amma Atiku dansu na biyu zai kasance.” In ji Babachir.
Saboda haka tsohon sakataren yana ganin Atiku Abubakar dan takarar babbar jam’iyyar hammaya, PDP, ‘yan arewa za su zaba a zaben 2023.