Daidai ya rage saura kwanaki 100 a yi zaɓen shugaban ƙasa, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta jaddada cewa ba za ta taɓa fasa bin sabon tsarin ta na tattara sakamakon zaɓe da tantance yawan ƙuri’u na BVAS da IReV ba, domin tabbatar da sahihin zaɓe.
Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Laraba, inda ya ce an bijiro da tsarin amfani da BVAS da IReV ne domin hana murɗiya, maguɗi da satar akwati lokacin gudanar da zaɓen 2023.
Yakubu ya yi wannan ƙarin haske ranar Laraba, cikin jawabin da ya fitar daidai saura kwanaki 100 cif kafin a yi zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya, wanda za a yi ranar 25 Ga Fabrairu 2023.
Za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na Majalisar Dokoki a ranar 11 Ga Maris, makonni biyu bayan zaɓen gwamna.
Kwanan nan wasu masu katsalandan sun yi ƙoƙarin kiran INEC da ta janye shirin yin amfani da na’urorin BVAS da IReV wajen tantance masu jefa ƙuri’a a lokacin da za a kaɗa ƙuri’u a zaɓen 2023.
Masu neman kada a yi amfani da BVAS da IReV sun ce gara a koma yin amfani da fallen takarda, wato fam wanda za a riƙa rubuta adadin ƙuri’un da kowane ɗan takara ko jam’iyya ta samu.
INEC ta daina amfani da wancan tsohon tsarin rubuta sakamako a fallayen takardu tun bayan ƙirƙiro tsarin BVAS da IReV, wanda ta ce da shi za ta yi amfani a zaɓen 2023.
A kan haka ne Yakubu ya ce tuni an shirya yin amfani da sabon tsarin a zaɓe mai zuwa, kuma ba za a fasa yin amfani da tsarin ba.
“Kamar yadda na sha nanatawa, INEC Nijeriya ta ke yi wa aiki, ba wata jam’iyya ko wani ɗan siyasa ba. ‘Yan Nijeriya mu ke wa aiki tare sadaukarwa. Saboda jama’a buƙatar sahihin zaɓe mai inganci, wanda zai zama karɓaɓɓe ta hanyar amfani da tsarin na’rorin fasaha, waɗanda za su tabbatar da cewa an yi bi sahihiyar hanyar tantance masu rajistar shaidar masu jefa ƙuri’a. Daga nan kuma za a loda sakamakon kai-tsaye daga rumfukan zaɓe zuwa shafukan rariyar tattara bayanan INEC, yadda kowa zai iya shiga ya duba sakamakon zaɓe tun a ranar da aka kaɗa ƙuri’a.
“Saboda haka dalili kenan aka ƙirƙiro BVAS da IReV. Kuma ba za mu fasa yin amfani da waɗannan tsare-tsare guda biyu ba a zaɓen 2023,” inji Yakubu.
Shugaban na INEC ya ce nan da makonni kaɗan hukumar sa za ta fara yin taron ganawa da manema labarai duk bayan sati biyu, domin ta riƙa sanar wa ‘yan Najeriya irin shirin da ta ke ciki dangane da tunkarar zaɓen 2023.
Ya ce idan zaɓen ya kusa ne INEC za ta riƙa yin taron zantawa da manema labarai a kowace rana.