Gwamnan Jihar Bauchi kuma dan takarar kujerar gwamnan Jihar na jam’iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad, ya ayyana mambar Majalisar wakilai ta tarayya da ke wakiltar mazabar Zaki, Honorable Muhammad Auwal Jatau a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 da ke tafe.
Honorable Jatau shi ne ya shelanta hakan a hirarsa da ‘yan jarida a Bauchi ranar Lahadi.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa Sanata Baba Tela shine mataimakin gwamnan Jihar a halin yanzu amma ba zai samu damar yin takara tare da gwamna Bala Muhammad ba a zaben 2023 sakamakon jingine shi a gefe da gwamnan ya yi.
Sabon abokin takarar ya gode wa gwamnan bisa zabinsa da ya yi a matsayin abokin da za su yi takara, sai ya sha alwashin yin kokari domin tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP a jihar.
A cewarsa Muhammad Auwal Jatau, “Zan yi amfani da wannan damar wajen mika godiya ta musamman ga Allah (subhanahu wataala) da kasancewa ta a halin da na samu kaina a yau mataimakin dan takarar gwamnan Jihar, zan kuma mika godiya ta musamman wa shi gwamnanmu Bala Abdulkadir Mohammed da ya ga cewa ni na cancanta na zama mataimakinsa na cancanci na zama wanda zan yi aiki a karkashinsa ya ce ni din nan ya aminta ya yi aiki da ni.”
“Babu wani abun da dan adam zai maka a duniya fiye da mutum ya ce ka zo ka kasance mai rike masa nan ka tallafa masa a lokacin da yake aiwatar da hidima irin ta jama’a, ta Gwamnati da ta mulki. Wannan abin godiya ne kuma ina cike da godiyan.
“Bahaushe ya ce zo mu ci tuwo ya fi tuwon dadi. Saboda haka ina mika godiya bisa amincewa da ni da ya yi bisa yarda a ya dauka ya daura min.”
Ya tabbatar da cewa wannan zabin da aka masa zai yi iyaka bakin kokarinsa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 tare da nasarar su, ya kuma ce zai yi biyayya wa gwamnan kuma zai kasance mai hakuri a kowani lokaci domin cimma nasarorin da aka sanya a gaba.
Da ya juya kan ayyukan gwamna Bala kuwa, ya misalta Gwamnatin Bala Muhammad a matsayin wacce ya shimfida ayyukan raya jihar fiye da kowace gwamnati da aka taba yi a jihar. Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa zango na biyu na mulkin Bala Muhammad za ta zarce na farko ta fuskacin shimfida ayyukan raya jihar.