Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, ya kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya gudanar da taron tattaki a jihar domin gwada farin jininsa.
Ganduje ya yi wannan magana ne kan yadda mutane suka yi fitar dango don mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AP, Bola Tinubu baya a jihar a safiyar ranar Litinin.
- ‘Yansanda Sun Ceto Matafiya 76 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Kaduna
- Kwamandojin ‘Yan Ta’adda, Ba’a Usman, Alhaji Ari, Da Wasu Da Dama Sun Mika Wuya Ga Sojoji
A cewar Gwamnan, da yawa daga cikin mabiya Kwankwaso a yanzu suna tare da APC.
“Don haka, idan Kwankwaso yana tunanin zai iya lashe zabe, to ya yi irin wannan tattaki, ya kwatanta abin da ya faru idan zai iya,” in ji Ganduje a wani shirin siyasar gidan talabijin na Channels a yammacin ranar Litinin.
Gwamna Ganduje ya kara nuna shakku kan batun siyasar Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya bayyana cewa yana ficewa daga wannan jam’iyya zuwa wata tare da rasa dimbin mabiyansa a tafiyar siyasa.
Gwamnan ya yi imanin cewa Shekarau ya bar mafi yawan mabiyansa a jam’iyyar APC da NNPP kuma ya ba da shawarar cewa babu wanda ya san matakin da tsohon Gwamnan zai dauka na gaba.