Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana wasu sharuda guda biyu ga jam’iyyun siyasa da ke son sauya ‘yan takara ko abokan takararsu na shugaban kasa.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na INEC, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan cikin wani shirin gidan talabijin na Channels, a ranar Juma’a.
- ‘Yan Sanda Sun Ceto Mahaifiyar Dan Takarar Sanatan Jigawa Da Aka Sace
- Zaben Fidda-Gwanin APC: A. A Jinjiri Ya Maka Bashir Machina Kotu
“Jam’iyyar siyasa ba za ta iya maye gurbin wanda aka zaba ba, sai a lokuta biyu: idan wanda aka zaba ya mutu. Ko kuma idan wanda aka zaba ya janye daga takarar.
“In har janyewa ce dole ne ya kasance akwai wasikar da wanda aka zaba ya rubuta wa jam’iyyar siyasa, wanda ke nuna cewa ya janye daga takarar, tare da rantsuwar rantsuwa.
Idan ba a manta ba jam’iyya mai mulki APC, ta sanar da cewar ta zabi Kabiru Ibrahim Masari a matsayin mataimakin Tinubu ma wucin gadi.
Kazalika ma jam’iyyar NNPP, ta zabi wanda zai yi Kwankwaso takarar mataimakin shugaban kasa na wucin gadi.
INEC ta bayyana sharudan ne ga jam’iyyun da ke da muradin sauya dan takara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp