Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC), ta kara wa’adin rajistar katin zabe wanda da farko ta yi niyyar rufewa daga 30 ga watan Yuni 2022.
Sai dai INEC ba ta bayyana sabon lokacin da ta kara na ci gaba da yin rajistar katin zaben ba.
- An Kashe Kasurgumin Dan Fashin Dajin Da Ya Addabi Mutane A Leren Jihar Kaduna
- ‘Yan Bindiga Sun Sace DPO A Kaduna
Shugaban hukumar, Farfesa Yakubu Mahmoud ne, ya bayyana hakan ga masu yi wa kasa hidima a Abuja, yayin wani taron kara wa juna sani kan muhimmanci zabe a ranar Lahadi.
Sai dak Yakubu ya ce ba su bayyana lokacin da za a daina rajistar katin ba, kamar yadda wasu rahotanni ke cewa za a rufe a watan Oktoban 2022.
Game da lokacin da suka kara, shugaban hukumar ya ce har yanzu ba su yanke matsaya ba, amma za su tattauna sannan su sanar da ‘yan Nijeriya abin da ake ciki.
Yakubu, ya roki ‘yan Nijeriya da su yi amfani da katin zaben ta inda ya dace, ba wai amfani da shi wajen bude asusun banki ba kawai.