Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta fara raba Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) a cikin Oktoba da kuma Nuwamba, tare da kakka:ɓe sunayen duk waɗanda suka yi rajista sau biyu ko fiye da haka.
Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar Zaɓe, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke lura da aikin rajistar katin zaɓe a ranar Asabar a Auka, Jihar Anambra.
Okoye, wanda shi ne mai lura da aikin rajistar katin zaɓe a jihohin Abiya, Anambra da Binuwai, ya ce INEC ta na aikin rajistar ne a tsanake, “ta yadda za a kakkaɓe sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da sau biyu kafin a buga katin shaidar rajistar zaɓe har a rarraba su cikin Oktoba da Nuwamba.”
Ya ce, “Dokar zaɓe kuma ta umarci INEC ta kafa sunayen waɗanda aka yi wa rajista a dukkan ƙananan hukumomi 774 da kuma Cibiyoyin Rajista 8,809 da ake da su a ƙasar nan, domin jama’a su tantance sunayen su kuma masu ƙorafe-ƙorafe su yi.
“Sannan kuma za a buga Katin Zaɓe na Dindindin (PVC), a loda su a motoci zuwa kowace ƙaramar hukuma.”
Okoye ya ja hankalin jama’a cewa ɓata lokaci ne a ce mutum ya je ya yi rajista, amma ya kasa karɓar katin zaɓen sa. “Saboda tilas sai da katin zaɓe ne kaɗai mutum zai iya jefa ƙuri’a.”
Ya ce waɗanda aka yi wa rajista tsakanin Janairu zuwa Yuni za su karɓi katin zaɓen su cikin Oktoba. Su kuma waɗanda aka yi wa rajista daga 1 zuwa 31 ga Yuli, za su karɓi nasu katin zaɓen cikin Nuwamba.
Hukumar Zaɓe ta bijiro da sabunta rajistar katin zaɓe ne saboda dalilai da dama, waɗanda su ka haɗa da: samun damar yin rajista ga duk wani ɗan Nijeriya da ya kai shekara 18 daga 2019 zuwa 2022. Saboda ta hanyar mallakar rajista ne kaɗai wanda ya cika shekara 18 bayan 2018 zai iya yin zaɓe.
Haka kuma wanda bai samu damar yin rajista ta katin zaɓe a 2018 ba, ya samu damar yi a wannan lokacin.