Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ce a ranar 31 ga watan Yuli 2022 ne za ta kammala aikin yin rajistar katin zabe.
Hukumar ta sanar da wannan matakin ne bayan hukuncin da babban kotun tarayya ta yanke a ranar Laraba kan wata kara da kungiyar kare hakkin bil Adama ta SERAP ta shigar na neman a kara wa’adin aikin rajistar.
A sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar INEC, Festus Okoye, ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, ya ce a cikin hukuncin na kotun dukkanin abubuwan da suke ba bisa ka’ida ba a tsarin rajistar katin zaben an cire su.
Ya ce a hakan an kara mako biyu kan ranar da aka ware domin rufe aikin.
“Kuma an kara tsawon lokaci a kowace ranar da za a ke aikin ne daga karfe 9 na safiya zuwa 5 na yammaci na kowace rana. A maimakon 9 na safiya zuwa 3 na rana da ake yi a baya.”
Okoye ya kuma ce hatta a ranakun hutu na Asabar da Lahadi duk za a ke gudanar da aikin.
Ya ce kuma aikin na gudana a dukkanin runfunan da ake aikin a sassan gundumomin da suke fadin kasar nan.
Ya kara da cewa tsare-tsaren da suke tafiya a kai suna taimaka musu wajen ganin sun fitar da karin jefa kuri’a na dindindin ga al’ummar kasa ga wadanda suka yi sabbi ko wadanda suka sabunta nasu domin samun damar su jefa kuri’a a zaben 2023.
Ya nemi al’ummar kasar nan da su yi hakuri wajen jiran fitar musu da katin zaben bayan sun yi rajistar ko sun sabunta katinan nasu.