Kakakin majalisar dokokin Kano, Hamisu Chidari ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na mazabar Dambatta/Makoda ba tare da hamayya ba.
Jami’in zaben fidda gwani na jam’iyyar, Aminu Sani ne ya bayyana hakan a Dambatta.
Sani ya bayyana cewa Chidari ya samu kuri’u 51 a karamar hukumar Makoda da kuri’u 47 a karamar hukumar Dambatta.
“Jimillar wakilai 105 ne suka kada kuri’unsu, Chidari ya samu kuri’u 98 yayin da kuri’u bakwai ba su da inganci. Hamisu Chidari da ya samu mafi yawan kuri’u an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani,” in ji shi.
Chidari a jawabinsa, ya godewa wakilan da kuma al’ummar mazabar Dambatta/Makoda a tarayya bisa amincewar da suka yi masa.
Shugaban majalisar ya yi kira ga sauran ‘ya’yan jam’iyyar da su ba shi hadin kai don ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a zaben 2023.
Ya kuma yabawa al’umar yankin bisa yadda suka gudanar da zaben cikin lumana.