Watanni takwas da suka rage a fara gudanar da zabubbukan kakar 2023, dimbin kalubalen rashin tsaro na ci gaba da yiwa wasu jihohin kasar nan daurin Damin-minta, musamman kalubalen ‘yan bindiga, rikici a tsakanin kabilu da ‘yan Boko Hram.
Wadannan kalubale za su iya shafar kokarin hukumar zabe ta kasa INEC wajen gudanar da zabubbukan musamman a wadannan jihohin da lamarin ya fi ta’azzara.
Jihohin dai sune, Kaduna, Nija, Katsina, Sakkwato, Benuwai da kuma Filato, inda kalubalen ka iya janyo hana wasu jefa kuri’un su a lokacin zabubbukan bana.
A wasu jihohin ta’addacin ‘yan bindigan daji ya raba al’ummomi da dama daga matsugunan su, inda a yanzu, suke gudun hijira a sansani daban-daban.
Wasu masana sunce, matukar Gwamnatin Tarayya ba ta dauki matakan gaggawa ta hanyar yin amfani da karfin soji ba, zaben ba zai gudana a yankunan ba.
Sai dai, hukumar zabe ta kasa INEC, ta bai wa ‘yan gudun hijra tabacin cewa, za su kada kuri’unsu a lokacin zaben.