A yau Laraba ne babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta yi watsi da karar da aka shigar a gabanta, inda ake kalubalantar tsaya wa takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa a jam’iyyar APC.
A cikin takardar karar mai dauke da lamba FHC/ABJ/CS/854/2022, Alkaliyar kotun Fadima Aminu Murtala ta danganta karar da dattijo Ngozika Ihuoma ya shigar a gabanta a matsayin kara mara inganci da bata da hujjoji.
Fadima Aminu, a saboda hakan, ta yi fatali da karar.
Ihuoma dai, ya maka Tinubu ne a gaban kotun tare da wasu mutane biyar a ranar 9 ga watan Yunin 2022 bayan da Bola ya lashe zaben fidda gwani a APC.