A zaman majalisar da aka gudanar a yau 9 ga Oktoba a zauren majalisar dokokin jihar Kano, an amince da karin kasafin kudin shekarar 2023, wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba ga ayyukan ci gaban jihar.
Zauren majalisar wanda shugaban majalisar, Rt Hon Jibril Ismail Falgore ya jagoranta, ya amince da karin kasafin ne bayan nazari sosai da kwamitocin majalisar baki daya suka gudanar.
- Masu Laifi 222 Sun Mika Wuya, An Cafke 98 A Kano
- Gwamnatin Kano Ta Shirya Yi Wa Dabbobi Miliyan 1.8 Rigakafi
Manufar wannan karin kasafin kudin ita ce, samar da tsarin kudi da ya dace don aiwatar da wasu ayyuka masu tasiri a fadin jihar, dai-dai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara).
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne ya mika kudurin kasafin kudin ga majalisar domin ta duba tare da amincewa tun kwanakin baya.
Karin kasafin kudin ya haura sama da Naira biliyan N58, an ware kashi 92 cikin 100 domin aiwatar da ayyukan raya kasa da walwalar al’ummar jihar yayin da aka ware ragowar kashi 8 domin gudanar da ayyuka masu bijirowa na yau da kullum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp