A ranar Talata ne hukumar kula da tashar jiragen ruwa na ‘Lekki Deep Seaport’ ta bayyana cewa, ta samu nasarar mu’amala da manyan jiragen ruwa 75,000, ta karbi wasu kananan jirage 25,000 haka kuma kwantaina 100,000 aka sauke a cikin shekarar data gabata.
Sanarwa haka ta fito ne daga bayanin da hukumar tashar ta yi a shafinta na D don murnar cika shekara 1 da fara harkokin kasuwanci a tashar, inda aka fara a ranar 1 gaa watan Afrilu 2023. An yi haka ne don kuma a duba yadda aka gudanar da aikin tashar a cikin shekara da ta gabata. Sanarwar ta ce, a cikin shekarar ne tashar ta karbi babban jirgi dauke da iskar gas ‘LNG-powered bessel’ mai nauyin 366 LOA.
- FCTA Ta Rushe Gidaje Dubu 15 Da Aka Gina Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Unguwar Gwarinpa Da Ke Abuja
- Kotu Ta Tsare Wani Mutum Kan Yi Wa ‘Yar Shekaru 11 Ciki A Legas
Haka kuma a 2023 tashar ta samu nasarar gudanar da harkokin karbar kayayyaki da aka fi sani da “Transshipment” har guda 25,000 daga watan Yuni 2023 zuwa yanzu.
Bayani ya kuma nuna cewa, tashar ta samu nasarar karbar kwantaina 100,000 ba tare da wata mastala ba, wannan ke kara nuna cewa, tashar a shirye take na shiga tsarin kasuwanci a duniya.
Tashar ta kuma mika godiya bisa goyon bayan da take samu daga Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA), ta kuma nemi a ci gaba da samun irin wannan hadin kan.
Daga nan sun mika godiya da jinjina ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da Ministan Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, Shugaban NPA, Mohammed Bello-Koko, Shugaban Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi da shugababn hukumar NEPZA, Dr. Olufemi Ogunyemi, da sauran su.
“Muna kuma mika godiya ga shugabanninmu, kamar Mr Biodun Dabiri, Alhaji Bode Oyedele, Mr Haresh Aswani, Mr Mohammed Bello-Koko, Mr Nabin Nahata, Mr Wu Di, Mr Steben Liu da Mr Dinesh Rathi a bisa goyon bayan da suke ba mu har muka samu wannan nasarar”.