- Hukumar Ta Warware Zare Da Abawa
- Ta Yi Gargadi Kan Daukar Aiki Na Bogi
- Akwai Katin Zabe Miliyan 6.7 Da Ba A Karba Ba
Ganin yadda wasu ‘yan siyasa suka dukufa sayen katin zabe daga masu kada kuri’a domin shirin ko-ta-kwana a zaben 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce duk masu yin haka sun yi a banza.
A cikin makon nan, hukumar ta (INEC) ta caccaki wadanda ke da hannu wajen sayen katin zaben da kuma wadanda ake amfani da su wajen tattara lambobin katin zaben na mutane.
Mai magana da yawun INEC, Festus Okoye ya bayyana cewa abin da masu sauen katin zaben ke yi zalunci ne ga masu kada kuri’a, domin ba zai amfane su da komai ba illa hana masu katin ‘yancinsu na zabe rumfunar zabe.
Okoye ya bayyana hakan ne a wani shirin safe na gidan talabijin na Arise, inda ya kara da cewa bayanan duk wadanda suka yi rajistar zaben yana kunshe a cikin na’urar tantance masu zabe ba wai a katin zabe ba.
Ya ce, “Wadanda suke tattara lambobin katin zaben mutane suna wahalar banza ne. Mai ya sa suke tattara lambobin katin zaben mutane da suka saya bayan a lokacin aka buga wadannan lambobobi a kananan hukumominmu da kuma wuraren rajistarmu sa’ilin da muke baje kolin wadanda suka yi rajistan masu zabe.
“Mun bayyana karara cewa wannan hukumar za ta tura katunan zabe ta na’urar tattance masu zabe domin tantance masu kada kuri’a, sannan bayanan dukkan wadanda suka yi rajistan zabe a kowacce runfar zabe da ke Nijeriya tana cikin naurar ba a katin zabe ba.
Abin da kawai kwamishinan zabe zai yi a ranar zabe shi ne, duba lambobi shida na karshen katin jefa kuri’arku wajen yin amfani da shi domin fitar da lambobin katin zabenku don neman tattara bayananku daga naurar tantance masu zabe. Wadanda ke sayen katin zabe da daukar lambobin katin na yin haka ne saboda zaluncin masu jefa kuri’a kawai. Kwai za su iya hana mai zabe zuwa rumfar zabe a ranar zabe, amma dangane da daukar katin zaben wani ya ba wa wani don kada kuri’a, ina mai tabbatar maka da cewa abu ne mai wuya.”
Da ya guya batun ma’aikata na wucin-gadi kuwa, Okoye ya ce, “Hukumar ta dauki ma’aikatan wucin-gadi miliyan 1.4 wadanda suka hada da masu bautan kasa da daliban babban makaranta da ke ajin karshe. Ka san cewa abu ne mai wahala hukumar INEC ta iya biyan ma’aikata miliyan 1.4 albashi. Gaba daya hukumar tana da ma’aikata 16,000, lokacin da muka fara bayar da katin zabe a yankuna daban-daban, mukan gayyato masu bautar kasa domin su taimaka wa hukumar wajen bayar da katin jefa kuri’a.”
Hakazalika, hukumar INEC ta gargadi yara da shekarunsu bai isa zabe ba su yi nesa da rumfunan zabe lokacin da ake gudanar da babban zaben 2023.
Mai magana da yawun hukumar INEC, Festus Okeye shi ya yi wannan gargadi lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels. Ya ce za a damke duk wani yaro da shekarunsa ba su isa zabe ba da iyayensa wadanda suka taimaka musu wajen gudanar da irin wannan mummunan lamari.
“Mun bayyana karara cewa duk wanda shekarunsa ba su isa zabe ba, ka da ya tunkari rumfunan zabemu a ranar zabe.
“Idan kuma mutum ya bayyana a wurin, za a kama mutum tare da iyayensa don taimakawa wajen irin wannan mummunan aikin,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi gargadi ‘yan Nijeriya kan daukan aiki na bogi ga ma’aikatan wucin-gadi kan zaben 2023.
Gargadin yana cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar da ke dauke da sa hannun Babban sakataren INEC, Mista Rotimi Oyekanmi da kuma Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Tun a ranar 7 ga watan Satumbar 2022, INEC ta bayyana cewa za ta daukan aiki na ma’aikatan wucin-gadi kan zaben 2023, inda ta bayar da adireshin ta kamar haka; (www.pres.inecnigeria.org), sannan a ranar Laraba 14 ga watan Satumbar 2022 da misalin karfe 8 na safe hukumar ta bude, yayin da aka rufe a ranar Laraba 14 ga watan Disambar 2022 da misalin 8 na yammaci.
Oyekanmi ya kara da cewa a yanzu haka ana ci gaba da yada rahotannin karya cewa hukumar na daukan aiki ga wadanda za su taimaka mata wajen zabe bayan kuma adireshin INEC a rufe yake.
Ya ce, “Adireshin da ake tallatawa na daukan aikin ma’aikatan bogi kan zaben 2023 ba gaskiya ba ne, domin a yanzu haka adireshin hukumar a rufe yake saboda ta kammala daukan aiki na ma’aikatan wucin-gadi.
“INEC ta rufe adireshin daukan aiki na ma’aikatan wucin-gadi tun a ranar 14 ga watan Disambar 2022.”
Akwai Katin Zabe Miliyan 6.7 A Jihohi 17 Da Ba Amsa Ba
Akwai ‘yan Nijeriya miliyan 6.7 da har yanzu ba su amsa katin zabensu ba duk da ya rage kasa da makonni a gudanar da babban zabe na 2023.
Bayanai daga ofisoshin INEC da ke jihohi a ranar Talata da ta gabata, sun nuna cewa akwai katunan zabe miliyan 6.7 a jihohi 17ciki har da Abuja da ba a amsa ba.
Hukumar INEC ta ayyana fara amsan katin zabe tun a ranar 12 ga watan Disambar 2022, inda za ta daina bayarwa a ranar 22 ga watan Janairun 2023.
Mai Magana da yawam INEC, Festus Okoye shi ya bayyana haka, wanda ya ce daga ranakun 6 zuwa 15 ga watan Janairun 2023 za a dakatar da bayar da katin zabe a gundumomi a mayar da amsar zuwa kananan hukumomi.
A lokacin zaben 2019, INEC ta ce tana da wadanda suka yi rajistan zabe miliyan 82, amma miliyan 28.6 kacal suka yi zaben shugaban kasa, inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri’u miliyan 15, inda ya doke Atiku Abubakar da ya samu kuri’u miliyan 11.2.
Bayanai daga ofishin INEC a Jihar Legas ya nuna cewa har zuwa ranar 29 ga watan Disambar 2022, akwai katunan zabe da suka kai 1,693,963 ba a amsa ba. Wannan yana cikin rahoton INEC ta Jihar Lagas da ta fitar.
“Tsofaffin kotunan zabe da ke shalkwatan hukumar sun kai 6,570,291, sannan tsofaffi katunan da aka amsa sun kai 5,653,330 zuwa ranar 29 ga watan Disambar 2022. Jimillar tsofaffin katunan zabe da ba a amsa ba sun kai 916,961, yayin da sabbin katunan da ba a amsa ba a shalkwatan hukumar sun kai guda 940,200, sababbin katin zaben da aka amsa yawansu ya kai guda 163,198 duk zuwa zuwa ranar 29 ga watan Disambar 2022.”
Bincike daga ofishin INEC a Abuja ya nuna cewa akwai katin zabe guda 460,643 wadanda ba a amsa ba zuwa ranar 24 ga watan Disamba.