Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta cimma nasara a aikin da ta yi na gwajin na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Mutane da dama sun jinjina wa hukumar dangane da nasarar da ta samu wajen aikin gwajin na’urar, wato BVAS.
Sun bayyana fatan cewa Allah ya sa a samu irin haka idan an zo yin amfani da na’urar a zaɓen 2023.
Waɗanda su ka layi aka yi masu gwajin sun ce lallai idan har haka na’urar BVAS ta ke, to za a samu gagarimar nasarar yin sahihin zaɓe kuma karɓaɓɓe a ranar 25 ga Fabrairu da kuma 11 ga Maris.
Da yawan su kuma sun haƙƙaƙe cewa babu yadda za a yi maguɗi, rinto ƙuri’u ko aringizo a zaɓen 2023.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce wannan aikin gwajin na’urar BVAS zai bai wa hukumar sa damar ganin inganci da nagartar aikin da BVAS ɗin zai yi, idan an zo zaɓen watan Fabrairu da Maris na wannan shekara.
A Jihar Katsina, an yi gwajin na’urar tun daga safe har zuwa ƙarfe 1 na rana.
Wakilin mu ya ce ya lura akwai jami’an tsaro da malaman zaɓe a inda aka yi gwajin a Ƙaramar Hukumar Katsina. Ya ce dukkan su sun isa da wuri, kamar yadda aka tsara.
Sauran wasu wuraren da ya je sun haɗa da Shinkafi A Gezawa, Sabuwar Bakuru, inda ya iske jami’an tsaro danƙam.
An tsara fara gwajin ƙarfe 8:30 na safe zuwa ƙarfe 2 na yamma a faɗin ƙasar nan.
Jami’an sun isa da wuri, amma ba su fara aikin ba sai ƙarfe 9 na safe.
Zuwa ƙarfe 1.25 na yamma, an tantance mutum 170, wasu 12 ba a tantance su ba.
Umaru Shehu daga Mazaɓar Shinkafi A ya shaida wa wakilin mu cewa ya yi matuƙar mamakin yadda tsarin tantance masu rajista da na’urar BVAS ke aiki lafiya ƙalau, ƙeƙe-da-ƙeƙe, kuma a cikin sauri.
“Saboda kwata-kwata ko minti biyu ban yi ba, na kammala komai,” inji shi.
INEC da kuma masu jefa ƙuri’a sun nuna gamsuwar su dangane da yadda aikin gwajin na’urar tantance masu rajistar zaɓe ya gudana a Gundumar FCT, Abuja.
Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya ziyarci wasu rumfunan zaɓen da aka yi tantancewar, ya ce hukumar sa ba ta samu rahoton kasawa, cikas ko tasgaro daga ko’ina ba.
INEC ta zaɓi wasu mazaɓu ne daga dukkan jihohin ƙasar nan da Abuja domin ta gudanar da aikin gwajin na’urar tantance masu rajistar zaɓe, wato BVAS, domin ƙara wayar wa da masu zaɓe kai dangane da aikin na’urar.
Hakan kuma zai ƙara sa jama’a amincewa da BVAS da kuma rungumar tsarin hannu biyu, ta hanyar yin amanna da sahihancin sa.
Yayin da ya ke duba yadda aikin gwajin ya riƙa tafiya, Yakubu ya nuna gamsuwar sa sosai da ingancin BVAS, ganin yadda ba a samu wani cikas ba.
“Maƙasudin wannan aikin tantancewar gwaji, shi ne domin a tabbatar da ingancin sa.
“A rumfunan zaɓe biyu da mu ka ziyarta, har yanzu ba mu samu rahoton wata matsala da aka fuskanta da BVAS ba. Na’urorin su na aiki sosai. Kuma irin wannan rahoton mu ke samu daga dukkan sasan kasar nan inda aka gudanar da gwajin.”
Yakubu ya ce duk inda aka gudanar da gwajin, an tanadi wasu na’urorin, waɗanda waɗanda za a ci gaba da aiki da su idan har wanda ake aiki da shi ya samu matsala. Ya ce a lokacin zaɓen na ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Oktoba, za a wadatar da BVAS wadatattun da za a iya amfani da wani daga cikin su ya samu mishkila.
Ya ce, “Kuma ko da wata na’urar ta samu mishkilar, to akwai ƙwararrun da za su gyara a cikin gaggawa.”
Shugaban na INEC ya ce, “Daga irin yadda wannan aikin gwaji ya tabbatar, an samu gagarimar nasara, kuma za a samu nasarar a zaɓen 2023, domin a cikin ƙasa da sakan 30 nau’arar BVAS ke tantance mai sahihiyar rajistar yin zaɓe mutum ɗaya.”
Ya ce kuma irin wannan rahoton INEC ta riƙa samu daga dukkan wuraren da aka gudanar da aikin gwajin a faɗin ƙasar nan.
Mutane da dama da aka tattauna da su, sun nuna gamsuwa da ingancin BVAS. Wani mai suna Nwani da ya ce shi ba a wannan rumfa ya yi rajista ba, ya ce ya je ne domin ya tabbatar da iƙirarin da INEC ta yi cewa BVAS ɗin da aka kai wannan rumfar zaɓe, ba zai tantance wanda ya yi rajista a wata rumfar zaɓe ba can daban ba.
“Ba a nan suna na ya ke ba. Na zo ne ganin-ƙwam. Kuma na bada kati na an duba, sai aka ce min ba a wannan rumfar zaɓen suna na ya ke ba.
“Aka saka kati na, amma na’urar BVAS ta ce, ‘a’a, babu sunan ka a wannan rumfar zaɓen.”
Yayin da BVAS ya ƙi tantance shi, a gaban sa na’urar ta riƙa tantance waɗanda sunayen su ke a rumfar zaɓen, wato ta Area 10, Abuja.