Sama da ‘ya’yan jam’iyyar PDP 12,000 ne a karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, tare da yin alkawarin mara wa jam’iyyar baya domin samun nasara a zaben 2023.
Wadanda suka sauya shekar da suka hada da tsohon kwamishina, shugabannin mata da matasa na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Giwa, sun samu tarba daga shugaban jam’iyyar APC na jihar, Emmanuel Jakada da dan takarar gwamnan jam’iyyar, Sanata Uba Sani a wani gangami da aka gudanar a karamar hukumar.
- Yawan Kayayyakin Da Masana’antu Sin Suka Samar Ya Karu Da Kaso 5 A Watan Oktoba
- Sojoji Sun Kashe Shugabannin ‘Yan Bindiga Buzu, Ganai Da sauransu A Harin Jirgin Yaki
A jawabinsa na maraba, Sani ya ce zarge-zargen da ake yi wa jam’iyyar PDP a jihar a kullum, wata manuniya ce cewa nan ba da jimawa ba babbar jam’iyyar adawa za ta ruguje tun kafin babban zabe.
Ya kuma bai wa wadanda suka sauya shekar dama a jam’iyyar APC, ba tare da la’akari da sabbin mambobi ne su ba, ya kuma shawarce su da su yi aiki tare da kada kuri’a ga dukkan ‘yan takarar APC a zaben 2023.
“Mun gamsu cewa karamar hukumar Giwa za ta zabi jam’iyyarmu ta APC kuma PDP ta mutu a nan. Muna farin cikin sanar da ku cewa mambobin PDP 12,870 ne suka sauya sheka zuwa APC a yau. Muna so mu tabbatar muku da cewa dukkanku muna maraba da zuwa babbar jam’iyyarmu. Muna farin cikin sanar da ku cewa shugabar mata ta PDP ta dawo gare mu,” in ji Sani. ..
A nasa bangaren, shugaban jam’iyyar APC, Emmanuel Jakada, ya yaba wa sabbin ‘ya’yan jam’iyyar bisa sauya shekar da suka yi, inda ya ce jam’iyyar ta kawo ribar dimokuradiyya ga al’ummar Jihar Kaduna.
“Mun ji dadin yadda al’ummar karamar hukumar Giwa suka fahimci cewa babbar jam’iyyarmu ta APC ce aka fi aminta da su, muna godiya ga sabbin mambobinmu kuma za mu yi aiki da su, muna kara musu kwarin gwiwa don samun karin jama’a su shigo jam’iyyar mu. Mun yi imani, a 2023, za mu lashe dukkan mukamai, “in ji shi.