Dan Takarar Shugaban kasa a karkashin Inuwar APC, Rochas Okorocha ya yi ikirarin cewa duk cikin ‘yan takarar babu Wanda zai iya kawo Kuri’u masu yawa irin yadda Buhari ya Kawo kamar shi.
Dan takarar wanda tsohon Gwamnan Jihar Imo ne, ya ce, ya samu yakinin haka ne sabida irin farin jininsa a siyasance a yankin Arewa ya fi yawa a kowane yanki.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci ranar Laraba, kan batutuwan da suka dabaibaye batun gudanar da zaben fidda gwani na kujerar Shugaban Kasa a APC. Kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Da aka tambaye shi kan cancantar shi ta tsayawa takarar, Rochas ya ce, “Tambayar da ya kamata APC ta yi wa kanta a yanzu ita ce wanne dan takara ne zai iya samo mata yawan kuri’u a Arewacin Nijeriya kamar yadda Buhari yake yi a baya?
“Duk wani abu koma-bayan haka son zuciya ne kawai. Saboda yanzu abin da kawai PDP take tutiya da shi, shi ne za ta samun tarin kuri’a daga Arewa. Wannan kuma gaskiya ne.
“Ina ganin ni ne dan takarar da APC zata bawa tutar Shugabancin kasa, sabida na fi farin jini a Arewa ma fiye da a kowane yanki,” inji shi.
A ranar 25 ga watan Mayu ce dai EFCC ta cafke Rochas Okorocha, wanda shi ne Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, a gidansa da ke Abuja.