Babban Faston da ke kula da cocin ‘Citadel Global Community Church’ da ke Legas, Pastor Tunde Bakare, ya nuna kwarin gwiwarsa na cewa, tabbas zai iya kayar da Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP a yayin babban zaben gama-gari na 2023 muddin jam’iyyar APC ta amince ta ba shi tikitin.
Faston a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida, .ai neman tikitin takarar shugaban kasan ya nuna gamsuwarsa da yadda aikin tantance’yan takaran shugaban kasa ke gudana.
“Aikin tantance ‘yan takara na gudana cikin kwanciyar hankali kuma na yaba da irin tambayoyin da suka min. Sun tambayeni ta wasu hanyoyi za mu iya bi wajen shawo kan matsalolin da suke addabar Nijeriya, na kuma amsa musu dukka.
“Da izinin Allah, muna da tilin abubuwan da muka shirya yi wa kasar nan. A irin wannan lokacin da muke cikin na mawuyacin hali da muka samu kanmu, ina da dukkanin hanyoyin shawo kansu.”
Ya ce, a shirye yake ya yi duk mai yiyuwa domin magance kalubalen da suke jibge.
Yana mai cewa muddin APC na son cikin dakika kalilai ta kada Atiku a zaben 2023 kawai ta ba shi tikiti domin a shirye yake ya kara da shi Kuma yana da kwarin guiwar zai yi nasara a kan Atiku.