Jam’iyyar PDP ta garzaya babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, inda ta nemi kotun ta hana Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da mataimakinsa Jatau Manassah Daniel, shiga a dama da su a zaben 2023 bisa zarginsu da gabatar da takardun bogi.
A kara mai lamba FJC/ABJ/CS/1301/2022 da ke tsakanin jam’iyyar PDP da wasu mutum biyu (masu kara) da INEC da wasu uku (wadanda ake kara) da aka shigar a ranar 2 ga watan Agustan 2022, PDP na rokon kotun da ta hana gwamna Inuwa da mataimakinsa yin takarar gwamnan jihar Gombe, kan zarginsu da mika takardun bogi ga INEC kuma aka wallafa a ranar 22 ga watan Yulin 2022.
A takardar sammacin da suka shigar ta hannun lauyiyinsu Cif Arthur Obi Okafor, (SAN) da J.J. Usman, (SAN), masu kara sun ce Inuwa da mataimakinsa, sun shigar da bayanai na karya da ake zargin suna amfani da takardun bogi ne.
Don haka ne suka nemi a hana su takarar bisa kafa hujja da cewa irin wannan batun ya saba wa sashe 177(d) da sashe 182(1) (j) na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).
A takardun kotun da wakilinmu ya samu, masu korafi sun yi zargin cewa, Jatau na amfani da sunayen daban-daban a takardar shaidar kammala Firamare (Manassah Jatau), shaidar kammala Sakandare ta (WAEC) (Daniel Manassah J), shaidar kammala Jami’ar Maiduguri (Manassah Daniel Jatau), shaidar kammala hidimar kasa (NYSC) (Daniel Manassah) ba tare da tantancewa ko hadawa da wata shaidar canja suna a cikin fom din EC-9 da ya mika wa INEC ba.
Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa a 2022 gwamna Inuwa l, ya gabatar da fom dinsa na EC-9 (takardar neman zama gwamnan Jihar Gombe), inda ya ce ya yi aiki a kamfanin zuba jari na jihar Bauchi a 1984 da kamfanin A.Y.U & Co.Ltd a tsakanin 1985-2003, sabanin yadda ya ce a 2018 a cewa ya yi aiki da kamfanin zuba jari na jihar Bauchi a 1985 da kuma A.Y.U & Co. Ltd a tsakanin 1980-1990.
A cewar masu shigar da karar, mataimakin Inuwa (Jatau), ya makala takardar shaidar bautar kasa mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Yuli, 1980, inda ya bayyana haka: “Wannan shi ne don tabbatar da cewa Daniel Manassah NYSC/Mad/79/6201 ya cika shekara guda na hidimar kasa daga ranar 1 ga watan Yuli, Agusta 1979 zuwa 31 ga Yuli 1980 bisa ga sashe na 11 na dokar hidimar matasa ta kasa (NYSC) mai lamba 24 na 1973.
Masu shigar da karar sun ci gaba da cewa, mataimakin gwamnan wanda ya yi ikirarin ya yi aiki da sojan Nijeriya tun daga watan Agustan 1979 zuwa Yuli 1980, ya mika takardar shaidar kammala NYSC, wanda ya nuna cewa ya fara yin hidimar kasa a watan Agustan 1979 kuma ya kammala, haka a watan Yuli 1979.
Masu karar sun kuma kara da cewa daga sakin layi D na Fom din EC-9 da Jatau ya gabatar wa INEC, ya yi ikirarin cewa ya yi aiki da rundunar soji daga watan Yulin 1979 zuwa watan Agustan 1980 kuma dalilinsa na barin aikin soja din a watan Yulin 1980.
Sun kara da cewa, Jatau ya ce ya fara hidimar kasa bayan da bar aikin soja a watan Yulin 1980 amma ya gabatar wa INEC shaidar NYSC da ke cewa ya fara hidimar kasa daga watan Agustan 1979 zuwa watan Yulin 1979 (ya kammala).
Masu karar sai suka hakikance kan cewa Fom din rantsuwa ta EC-9 da gwamna Inuwa da mataimakinsa Jatau suka gabatar akwai bayanai na karya da dama a ciki ko kuma sun gabatar da takardun bogi don haka ba su cancanci shiga takarar siyasa ba.
Masu shigar da karar sun roki kotun ta gaggauta tsaida Inuwa da Jatau daga shiga a dama da su a neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a 2023.
Sai dai kotu ba ta sanya ranar fara sauraron karar ba zuwa yanzu.