• Leadership Hausa
Friday, June 2, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NBC Ta Ci Tarar Trust TV Tarar Miliyan 5 Kan Yada Ayyukan ‘Yan Bindiga 

by Sadiq
10 months ago
in Labarai
0
NBC Ta Ci Tarar Trust TV Tarar Miliyan 5 Kan Yada Ayyukan ‘Yan Bindiga 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar da ke kula da ayyukan kafafen watsa labarai (NBC), ta ci tarar gidan talabijin na Trust (Trust TV) Naira miliyan biyar saboda watsa ayyukan ‘yan ta’addan jihar Zamfara.

Hukumar, a wata takarda mai dauke da sa hannun darakta-janar dinta Balarabe Shehu Illela, ta ce ta ci tarar Trust TV ne saboda ta watsa rahoto na musamman da ya saba ka’idojin hukumar.

  • 2023: PDP Ta Bukaci A Hana Gwamnan Gombe Da Mataimakinsa Takara Kan Zargin Gabatar Da Takardun Bogi
  • 2023: Fintiri Ya Zabi Mace A Matsayin Abokiyar Takararsa

Sai dai kamfanin Media Trsut ya ce a “Yayin da muke ci gaba da nazari kan matakin hukumar da kuma duba zabukan da muke da su, muna sanar da cewa a matsayinmu na gidan talbijin, mun yi amannar cewa muna aiki ne domin al’umma ta hanyar karin haske kan batun garkuwa da mutane mai sarkakiya da kuma yadda yake shafar miliyoyin jama’ar kasarmu.”

Sanarwar ta kara da cewa rahoton ya bi salsalar zaman dar-dar a tsakanin al’umma da kuma abubuwan da suka sanya rikicin da ya sa wasu ke daukar makamai da ke jefa mutane cikin mawuyacin hali.

Rahoton ya fito da matsalolin rashin adalci da kabilanci da rashin iya gudanar da mulki wadanda su ne ke haddasa irin wannan rikici.

Labarai Masu Nasaba

Shawarwarin Tsohon Shugaban Kasa Babangida Ga Tinubu

Tinubu Ya Yi Alkawarin Inganta Mafi Karancin Albashin Ma’aikata

Hakazalika ya bayar da shawara kan yadda za a magance matsalolin ta hanyar tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed, da Sanata Saidu Mohammed Dansadau, da Farfesa Abubakar Saddique na Jami’ar Ahmadu Bello, da sauransu.

A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da matakin da BBC da kuma Trust TV suka dauka na watsa rahoton na musamman kan ayyukan ‘yan bindiga.

Tags: Ayyukan 'Yan BindigaBBCGidan TalabijinMiliyan BiyarNBCTaraTrust TV
ShareTweetSendShare
Previous Post

2023: PDP Ta Bukaci A Hana Gwamnan Gombe Da Mataimakinsa Takara Kan Zargin Gabatar Da Takardun Bogi

Next Post

Za A Gudanar Da Taron Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Na Duniya Na Shekarar 2022 A Shanghai

Related

Shawarwarin Tsohon Shugaban Kasa Babangida Ga Tinubu
Labarai

Shawarwarin Tsohon Shugaban Kasa Babangida Ga Tinubu

4 hours ago
Tinubu Ya Yi Alkawarin Inganta Mafi Karancin Albashin Ma’aikata
Labarai

Tinubu Ya Yi Alkawarin Inganta Mafi Karancin Albashin Ma’aikata

4 hours ago
Tinubu Ya Gana Da Makinde, Wike Da Ibori
Manyan Labarai

Tinubu Ya Gana Da Makinde, Wike Da Ibori

6 hours ago
Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur
Manyan Labarai

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

8 hours ago
Takaddama Kan Shirin Daukar Sabbin ‘Yansanda
Labarai

Yadda Matashi Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 10 Fyade A Bauchi

9 hours ago
Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa

10 hours ago
Next Post
Za A Gudanar Da Taron Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Na Duniya Na Shekarar 2022 A Shanghai

Za A Gudanar Da Taron Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Na Duniya Na Shekarar 2022 A Shanghai

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Jaddada Bukatar Gina Kasar Sin Mai Wayewar Kai Ta Zamani

Xi Jinping Ya Jaddada Bukatar Gina Kasar Sin Mai Wayewar Kai Ta Zamani

June 2, 2023
Kasar Sin Ta Bayyana Korafinta Dangane Da Yarjejeniyar Cinikayya Da Aka Kulla Tsakanin Amurka Da Taiwan

Kasar Sin Ta Bayyana Korafinta Dangane Da Yarjejeniyar Cinikayya Da Aka Kulla Tsakanin Amurka Da Taiwan

June 2, 2023
Taron Tattaunawar Shangri-La Ya Nuna Ra’ayin Tabbatar Da Zaman Lafiya Na Sin

Taron Tattaunawar Shangri-La Ya Nuna Ra’ayin Tabbatar Da Zaman Lafiya Na Sin

June 2, 2023
Shawarwarin Tsohon Shugaban Kasa Babangida Ga Tinubu

Shawarwarin Tsohon Shugaban Kasa Babangida Ga Tinubu

June 2, 2023
Tinubu Ya Yi Alkawarin Inganta Mafi Karancin Albashin Ma’aikata

Tinubu Ya Yi Alkawarin Inganta Mafi Karancin Albashin Ma’aikata

June 2, 2023
Yadda Aka Kammala Gasar Firimiya Ta Bana

Yadda Aka Kammala Gasar Firimiya Ta Bana

June 2, 2023
An Dakatar Da “Wasan Matsorata” Da Jam’iyyun Siyasan Amurka Suke Yi Amma Damuwa Ta Dore

An Dakatar Da “Wasan Matsorata” Da Jam’iyyun Siyasan Amurka Suke Yi Amma Damuwa Ta Dore

June 2, 2023
Tinubu Ya Gana Da Makinde, Wike Da Ibori

Tinubu Ya Gana Da Makinde, Wike Da Ibori

June 2, 2023
RCEP Ta Fara Aiki A Kasashe 15 Da Suka Sa Hannu Kan Yarjejeniyar

RCEP Ta Fara Aiki A Kasashe 15 Da Suka Sa Hannu Kan Yarjejeniyar

June 2, 2023
Da Gaske Biyayya Ga Miji Tana Gaba Da Biyayaya Ga Iyaye?

Da Gaske Biyayya Ga Miji Tana Gaba Da Biyayaya Ga Iyaye?

June 2, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.