A yau Laraba Jam’iyyar PDP za ta baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alh. Atiku Abubakar, satifiket din shaidar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Taron wanda zai gudana a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, taron zai samu halartar gwamnonin jam’iyyar da mambobin jam’iyyar daban-daban, kamar yadda sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Hon Debo Ologunagba, ya bayyana a jiya cikin wata sanarwa.
- Da Diminsa: PDP Za Ta Sake Sabon Zaben Fidda Gwani Na Gwamnan Bauchi
- Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Shugabancin Jam’iyyar APC Ta Kasa
Atiku ya sake zama dan takarar PDP a karo na biyu cikin shekaru hudu, a filin wasa na MKO Abiola na kasa da ke Abuja da yammacin ranar Asabar, inda ya samu kuri’u 371 inda ya kuma doke abokin hamayyarsa, Gwamna Nyesom Wike wanda ya samu kuri’u 237.
Tun daga samun nasarar ya koma kwantar da hankalin ‘yan Jam’iyyar da kai masu ziyara bayan nasarar da ya samu. Atiku ya gana da manyan masu neman tikitin jam’iyyar wato gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki; Gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanual; da tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim.
Tsohon mataimakin shugaban kasar da kansa ya je gidajen ‘yan takarar da ke Abuja a wani mataki na neman goyon bayansu gabanin babban zabe.
Atikun ya kuma gana da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, inda suka yi masa godiya bisa janyewa daga takararsa tare da rokon magoya bayansa da su zabe shi (Atiku).