Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ya ayyana cewa yana goyon bayan zabin da jam’iyyar APC ta yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takararta na zaben 2023 dari bisa dari.Â
Wannan batun na kunshe ne cikin rubutaccen amsa da shugaban ya yi wa tambayoyin da Bloomberg News suka masa.
- Masu Garkuwa Sun Saki Tsohon Sakataren NFF, Hakimin Kauyen Zira Da Wasu
- Dimbin Kamfanonin Ketare Sun Yi Amanna Da Kasuwar Kasar Sin
Da aka tambayeshi idan zai fitar da dan takaran shugaban kasa wa zai zaba? Sai Buhari ya amsa da cewa, “Kwarai. Zan zabi dan takaran shugaban kasa na APC ne.
Da ya ke kuma kare takarar da gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele ya yi a kwanakin baya, Buhari ya ce, Emefiele ya fuskanci zarge-zarge ne don yana matsayin gwamnan banki kuma shi din bai ba tsarin tafiyar da tattalin arziki ba.
A cewarsa, “Shugaban kasa ne ya nada gwamnan bankin CBN. Amma nadin nasa ya samu ne da tabbatarwar Majalisar Dattawan Nijeriya.
“Daga nan, Majalisar daraktocin CBN ne za su tantance da tabbatar da ko matakin da gwamnan CBN din ya dauka ya ci karo da wasu dokokin don tabbatar da zai iya gudanar da ayyukan da suke gabansa yadda ya kamata.”