An kaddamar da taron koli na uku na kamfanonin kasa da kasa a cibiyar tarukan kasa da kasa ta birnin Qingdao da ke gabashin kasar Sin a ranar 19 ga wata, wanda ya samu halartar shugabanni fiye da dari daya daga kamfanoni 500 mafi karfin takara da kamfanonin da ke sahun gaba.
Wasu shugabannin kamfanonin sun bayyana cewa, ko da annobar COVID-19 tana haifar da wasu illoli, amma ana gudanar da ayyukan kamfanoninsu yadda ya kamata. Suna da imani da makomar kasuwar kasar Sin.
Alkaluman ma’aikatar kasuwancin kasar Sin sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Mayun bana, yawan kudaden ketare da kasar Sin ta yi amfani da su ya kai kudin Sin Yuan biliyan 564.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 84.1, wanda ya karu da kashi 17.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.
Kamfanin samar da magunguna na DOW na kasar Amurka yana halartar taron har shekaru uku a jere. A bana, shugabansa Jon Penrice ya halarci taron ta kafar bidiyo. Yana ganin cewa, kasar Sin na da babbar kasuwa, da sirrin ci gaba, da yawan bukatun masu sayayya, da cikakken tsarin masana’antu da tsarin samar da kayayyaki, idan an kwatanta da sauran kasuwanni. Duk wadannan sun samar da babbar dama ga kamfanonin kasa da kasa ciki har da kamfaninsa na Dow. Shi ya sa ba za su canja alkawarin da suka yi wa kasuwar kasar Sin ba, ko da yaushe suna da cikakken yakini da kasuwar Sin.(Kande Gao)