Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Bola Tinubu, ya fi shi lafiya.
Shettima, ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wani shiri na kai-tsaye ta Facebook, mai taken “Fashin Baki”, wanda Bulama Bukarti, Nasir Zango, Abba Hikima da Jaafar Jaafar su ke shirya.
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga Tare Da Bindige 1 A Jihar Katsina
- Ministan Wajen Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Amurka Ta Wayar Tarho
Jama’a na nuna damuwa kan yanayin lafiyar dan takarar na APC, inda wasu ke cewa bai cancanci zama shugaban kasa ba.
Sai dai Shettima, ya ce Tinubu ya ma fi shi lafiya domin ba shi da ciwon suga ko hawan jini.
“Bari na fada muku karara cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mutum ne mai lafiya garau ya ke.
“A ajiye siyasa a gefe, Tinubu na da lafiya a jiki da kuma karfin tunani da zai iya rike Nijeriya.
“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fi ni koshin lafiya kasancewar ni ina da ciwon suga da hawan jini, wanda shi kuma ba shi da shi.
Ko da ma cutar da mutane suka yi magana game da ita, rashin barci ne kawai. Da zarar ya samu isasshen barci, zai zama ya yi garau.
“Shugabanci ba kamar aikin karfi na daukar buhunan siminti ba ne. Yawanci aiki da kwakwalwa ya fi yawa a kan da jiki.
“Tsofaffin shugabannin kasa, Theodore Roosevelt da Abdelaziz Bouteflika da Daniel Arap Moi na Amurka da Algeria da Kenya sun jagoranci kasashensu ta hanyar bunkasar tattalin arziki yayin da suka dinga amfani da keken guragu,” in ji Shettima.
Tinubu ya sha suka kan yanayin lafiyarsa, lamarin da ya sanya abokan hammata ke masa adawa da lamarin.