Wata kungiya mai rajin inganta mulkin demokradiyya a Arewa Maso Gabas wato (North East Alliance for Democratic Change) ta sha alwashin kaddamar da asusun tallafin naira biliyan guda (N1b).
Kungiyar zata tara kudaden ne domin tara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin gudunmawa domin taimaka masa wajen yakin neman zaben 2023.
- Atiku Da Tinubu Sun Fara Cacar Baki Kan Zaben 2023
- Atiku Da Tinubu Sun Fara Cacar Baki Kan Zaben 2023
Shugaban kungiyar Lawal Muktar Ladan (Lawal Bauchi) ne ya shaida hakan a ganawarsa da ‘yan jarida a garin Abuja, ya na mai cewa za su yi hakan ne domin bada tasu gudunmawar wajen ganin Atiku ya samu nasarar zama Shugaban Kasa cikin sauki.
Lawan ya kara da cewa, sun yi imanin zaman Atiku shugaban Nijeriya alkairi ne, musamman ga ‘yan Arewa Maso Gabas da shiyyar Arewa da Nijeriya baki daya. Don haka ne suka ga dacewar kafa asusun da nufin ba shi agaji don cimma manufar da aka sanya a gaba.