Kwanaki kalilan da shiga sabuwar shekarar 2025, sabbin hare-haren ‘yan ta’adda, ‘yan fashin daji da sauran ayyukan ta’addanci ya zama wani abu na tura razani a zukatan al’umma a sassa daban-daban na kasar nan.
A cewar rahotanni, sama da mutum 78 ne aka kashe, yayin da kuma aka yi garkuwa da wasu mutum 80 a sassan jihohi daban-daban a mako na farko na watan Janairun 2025.
- Ranar Tunawa Da Mazan Jiya: Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Inganta Rayuwar Iyalan Jaruman Da Suka Rasu
- Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Kai Kashi 34.80 A Disamban 2024 – NBS
A ranar Asabar 4 ga Janairu, kusan sojoji takwas aka kashe a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a sansanin sojoji da ke Sabon Gari a karamar hukumar Dambo ta Jihar Borno.
Kazalika, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Argungu da ke Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum biyu, lamarin da kakakin ‘yansandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwarsa.
Wani karin abun takaici shi ne, yadda aka samun labarin kai hari a Charanci, Safana, Kurfi, da karamar hukumar Kaita a jihar Katsina, inda aka kashe sama da mutum 30 a tsakanin ranar Talata zuwa Alhamis.
An labarto cewa ‘yan bindiga ne suka farmaki mutanen a lokacin da suke dawowa daga ta’aziyya a karamar hukumar Batsari.
Haka kuma, ‘yan fashin daji sun kaddamar da munanan hare-hare a Jihar Borno da Kebbi, sannan wasu ‘yan bindiga da ba gano su waye ba da ke sheke ayarsu a yankin Umuokanne da ke Jihar Imo sun kashe mutane uku.
‘Yan awannin da harin Umuokanne, wasu ‘yan bindiga sun kaddamar da wani mummunar hari a Orsu ta Jihar Imo, inda mutum 18 suka rasa rayukansu.
A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar ta’addan Lakurawa ne sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel guda biyu da wani mazaunin kauyen Gumki da ke karamar hukumar Arewa ta Jihar Kebbi a karshen mako.
An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun mamaye al’ummar da ke tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, bayan da suka samu labarin cewa kamfanin sadarwa na kafa wata kafa ta sa ido a yankin.
Wasu mutane 11 kuma aka kashe a kauyen Gululu da ke Jahun da Miga. Sannan a ranar Laraba 8 ga Janairu, ‘yan bindiga sun mamaye kauyen Idu da ke gundumar Kufana a karamar hukumar Kajuru tare da kashe mutum 2. A kuma wannan ranar an kashe jami’ai guda 2 a wani harin da ‘yan Boko Haram suka kai a caji ofis din ‘yansanda da ke Borno.
Haka zalika, an ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani manomi mai suna Terzungwe Shaku a kauyen Akor da ke karamar hukumar Guma a Jihar Benuwai.
Shaku, wanda kuma ya mallaki wurin shan giya a kasuwar Akor, an sace shi ne jim kadan kafin sabuwar shekara kuma aka yi garkuwa da shi sama da makonni biyu kafin a kashe shi.
Mazauna yankin sun ce da farko masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 20, amma dangin sun tattauna kan naira miliyan 5.4, inda suka amince kuma iyalan suka biya.
Mutane da dama ne suka biya kudin fansa domin ceto ‘yan uwansu daga garkuwar da ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan uwansu.