Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi alƙawarin magance hauhawar farashin kayan abinci da magunguna da ake fama da su a faɗin ƙasar nan.
Ya ce zai yi haka ne ta hanyar ƙaddamar da sabon kamfanin bayar da lamuni don bunƙasa sarrafa kayan buƙatun yau da kullum a cikin gida.
A saƙonsa na sabuwar shekara ga ‘yan Nijeriya a ranar Laraba, shugaban ya bayyana cewa wannan kamfani zai taimaka wajen samar da kayan abinci da magunguna masu rahusa a kasuwanni.
Ya ce ana sa ran kamfanin zai fara aiki kafin ƙarshen zangon biyu na shekarar 2025.
Shugaban ya bayyana cewa wannan shiri haɗin gwiwa ne tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya da suka haɗa da Bankin Raya Masana’antu (BOI), Hukumar Lamunin Masu Sayen Kaya (NCCC), Hukumar Bunkasa Kadarorin Gwamnati (NSIA), da Ma’aikatar Kuɗi tare da goyon bayan kamfanoni masu zaman kansu da na ƙasa da ƙasa.
A cewarsa, “Sabuwar shekara ta zo da fatan alheri da burace-burace na kyautatuwar rayuwar ‘yan Nijeriya. Da yardar Allah, shekarar 2025 za ta kasance shekara ta cikar manyan burukanmu.”