LEADERSHIP ta ruwaito cewa masu neman takarar shugaban kasa a karkashin hadakar jam’iyyar ADC za su sanya hannu a kan yarjejeniyar tallafa wa duk wanda ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Wannan yarjejeniya ce da ‘yan takara suka cimma, amma duk da haka, dole ne su gudanar da zaben fid da gwani a tsakaninsu.
Tsohon ministan sufuri da kuma babban jigo a hadakar jam’iyyar, Rotimi Amaechi, ya bayyana wa LEADERSHIP hakan yayin wata tattaunawa da shi.
Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar, Sanata Dabid Mark, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da wanda ta fi so a matsayin dan takara kuma ya tabbatar da cewa a karkashin shugabancinsa, jam’iyyar za ta kai ga nasara.
Mark ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da wasu manyan mambobin hadin gwiwa suke matsa kaimi kan neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana burinsa na tsayawa takara a 2027, yayin da yake karban bakuncin tawagar masu ruwa da tsaki daga Gombe a gidansa da ke Abuja a ranar Asabar da ta gabata. Daga bisani, ya musanta cewa ya halarci wani taron da aka matsa masa lamba don ya janye kudirinsa na takara ga yankin kudu.
Haka shi ma, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa, yana mai cewa bai tattaunawa da kowa don ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a 2027 ba.
Yayin da magoya bayan ‘yan takarar shugaban kasan guda biyu da suka tsaya takara tare a 2019 ke karfafa gwiwar fitowar takarar shugaban kasar Nijeriya, musamman a shafukan sada zumunta, tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi, shi ma ya bayyana aniyarsa ta sake yin takara a zaben shugaban kasa a 2027 karkashin tutar jam’iyyar ADC.
Ya taba takarar shugaban kasa bai samu nasara ba a jam’iyyar APC a 2023, wanda Shugaba Bola Tinubu ya doke shi a zaben fid da gwani. Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana a cikin wata hira cewa ba ya da burin za ma shugaban kasa a halin yanzu.
Amma shi kuwa tsohon dan takarar shugaban kasa na ADC, Dumebi Kachikwu, ya zargi cewa jam’iyyar a karkashin sabuwar jagoranci, tana shirin ba da tikitin ta ga dan arewa, musamman ga Atiku.
Ya yi wannan zargin ne a daidai lokacin da ake zazzafar muhawara kan bayar da takarar shugaban kasa a yankin kudu ko arewa.
Wannan muhawara ta kasance daya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi zaben shugaban kasa na 2023 wanda Shugaban kasa Bola Tinubu na APC ya lashe, wanda ya sanya tikiti ya koma yankin kudanci bayan mulkin shekaru takwas na shugaban kasa Muhammadu Buhari daga arewa.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, Amaechi ya bayyana cewa yarjejeniyar tallafa wa duk wanda ya samu nasarar zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar za ta maida hankali ne kan fahimtar juna game da abin da za a kira gudanar sahihin zaben fid da gwani.
Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya ce, “Abin da muka yarda a zahiri shi ne, dole ne in ce akwai bukatar a bayyana al’amarin abin da muka yarda shi ne na cewa duk wanda ya zama dan takarar shugaban kasa bisa yadda aka gudanar da sahihin zaben fid da gwani, to dole ne dukkanmu mu mara masa baya.
“Abu na farko shi ne, dole ne mu zauna mu fayyace abin da muke nufi da sahihin zaben fid da gwani, saboda yana da sauki ga wani ya sauya tsarin kuma ya kira shi da suna sahihin zaben fid da gwani,” in ji shi.
Kazalika, sakataren yada labarai na ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa ba ya san da irin wannan yarjejeniyar ba.
Sakataren yada labaran jam’iyyar ya ce duk da haka jam’iyyar za ta yi iya bakin kokarinta wajen yi wa masu neman takara adalci a dukkan wani mataki.
Bolaji ya ce, “Ba na da masaniya game da wani yarjejeniya a tsakanin ‘yan takara. Abin da jam’iyya ta kudiri niyya shi ne, samar da kyawawan yanayi ga wani dan takara tare da yin adalci a tsananinsu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp