• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Ba Mu Kafa Haɗakarmu Don Cika Burin Atiku Ba – ADC

by Sadiq
3 months ago
ADC

Jam’iyyar ADC ta ce haɗakar da ake yi ba don mara wa tsohon mataimakin shugaban kas5a, Atiku Abubakar, baya ba ne a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

  • Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
  • Rikicin Makiyaya Da Manoma: An Kashe Mutum Daya, Gidaje 31 Sun Kone A Abuja

Ya ce wasu mutane ne ke yaɗa jita-jitar cewa ADC na goyon bayan Atiku domin su hana haɗakar yin nasara.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da ɗan takara da ta ke mara wa baya a yanzu.

“ADC ba jam’iyyar Atiku ba ce. Wannan ba haɗakar Atiku ba ce kwata-kwata.”

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

Abdullahi ya ce tun kafin a kafa haɗakar, wasu sun riga sun fara yaɗa cewa an shirya ta ne domin Atiku.

Ya ƙara da cewa: “Ni ina da shekara 56, wa ya ce ba zan iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba?”

Da aka tambaye shi game da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Abdullahi ya ce Obi na cikin haɗakar har yanzu.

Amma ya ce bai zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC ba har yanzu.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta bai wa Obi da kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dama su fice daga jam’iyyunsu na yanzu wato LP da SDP.

Ya kuma ce Obi ba zai koma jam’iyyar PDP ba, duk da cewa jam’iyyar tana ƙoƙarin jawo ‘yan siyasa domin dawo da ƙarfinta.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya za su yadda da jam’iyyarsu, Abdullahi ya ce jam’iyyar APC da ke mulki ta yi alƙawarin kawo sauyi amma ta gaza.

Don haka, ya ce lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su gwada wata sabuwar tafiyar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Labarai

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru
Wasanni

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Next Post
An Yanke Wa Mai Gadi Da Mai Dafa Abinci Hukuncin Kisa Kan Kashe Tsohon Kwamishina A Katsina

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.